A ranar Talata ne kasar Sin ta harba tauraron dan Adam mai dauke da na’urar bincike ta Chang’e-5, a wani aiki da ya kasance mafi sarkakiya cikin jerin ayyukan binciken duniyar wata da kasar ta aiwatar. A hannu guda kuma, ta sha alwashin raba samfuran sinadarai da tauraron zai dawo doron duniya dauke da su, tare da sauran sassa.
Chang’e-5, na’ura ce da aka kera domin sauka a yankin arewa maso yammacin “Oceanus Procellarum”, wanda ke kusa da gefen wata a farkon watan Disamba dake tafe. Ana kuma sa ran za ta dawo doron duniya da kimanin kilogram 2 na sinadarai.
Idan har wannan aiki ya yi nasara, zai kasance irin sa na farko da ya kunshi saukowa da sinadarai daga duniyar waya, tun bayan wanda Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet suka gudanar, a shekarun 1960 da 1970.
Duba da muhimmancin hakan ta fuskar binciken kimiyya, Sin ta sha alwashin raba sinadaran da na’urar za ta dawo da su doron duniya da sauran masu bincike. Kasancewar binciken sararin samaniya aiki da ke shafar rayuwar daukacin bil Adama, Sin na fatan bunkasa shi ta hanyar musaya, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. (Saminu)
Sanya Takunkumi Kan Pompeo Da Sauran Wasu Amurkawa 27 Abu Ne Da Ya Dace
Kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta sanar da sanya takunkumi...