Sin Na Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Kan Batutuwan Da Suka Shafi Palasdinawa

Daga CRI Hausa

Karamin jakadan kasar Sin dake ofishin MDD a Geneva, Jiang Duan, ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan yi wa Palasdinawa adalci da mayar musu halaltattun hakkokinsu.

Jiang Duan ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da aka tattauna kan yanayin hakkin bil adama a yankin Palastinu da aka mamaye, yayin taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo na 47.

A cewar jakadan, rikicin da ya faru tsakanin Palasdinu da Isra’ila a kwanakin baya, ya haifar da hasarar rayuka mai tsanani.

Kasar Sin tana sukar daukacin ayyukan nuna fin karfi, kuma tana kira ga Isra’ila da ta daina wargaza gidajen Palasdinawa ko korarsu daga muhallansu, kana ta daina gina sabon matsuguni.

Haka kuma tana kira ga Isra’ila ta martaba yanayin tarihin wurin ibada na birnin Kudus, ta kuma soke katangar da ta yi a zirin Gaza, ta yadda za a tabbatar da halaltattun hakkokin Palasdinawa.

Ya kara da cewa, ya dace al’ummun kasashen duniya su yi kokarin ingiza dakatar da bude wuta tsakanin sassan biyu, domin sassauta yanayin jin kai a Palasdinu, musamman ma a zirin Gaza, da cimma burin sake yin shawarwarin zaman lafiya a tsakaninsu, bisa tushen ‘shirin kasashe biyu’.

Bugu da kari, Jiang Duan ya ce a ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan yi wa Palasdinawa adalci, kana tana son ci gaba da ba da gudummowarta tare da sauran kasashen duniya domin shimfida zaman lafiya mai dorewa daga duk fannoni a yankin Gabas ta Tsakiya tun da wuri.”(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version