Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce Sin na maraba da masu zuba jari na sassan kasa da kasa, da su shigar da jarinsu cikin kamfanonin fasaha na Sin.
Pan Gongsheng, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Alhamis din nan, a gefen zaman majalissar wakilan jama’ar kasar Sin na 14 dake gudana, yana mai cewa, a daya hannun kasar Sin na adawa da matakan siyasantarwa, da yin matsin lamba a harkokin da suka shafi zuba jari a kasuwanni, da ma kafa wasu shingaye na rashin adalci a fannonin zuba jari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)