Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Sin Na Samarwa Kasashe 80 Da Kungiyoyin Kasa Da Kasa 3 Tallafin Rigakafin COVID-19

by Sulaiman Ibrahim
March 30, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Sin Na Samarwa Kasashe 80 Da Kungiyoyin Kasa Da Kasa 3 Tallafin Rigakafin COVID-19
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin na samarwa kasashe 80, da kungiyoyin kasa da kasa 3 tallafin rigakafin COVID-19. Kaza lika Sin na samarwa sama da kasashe 40 rigakafin, tana kuma hadin gwiwa da karin wasu kasashen sama da 10, a fannin binciken rigakafi, da samarwa da kuma sarrafa shi.
Hua Chunying ta yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na yau Talata, bayan da a jiya Litinin, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewa, akwai wagegen gibi a fannin gudanar da rigakafi tsakanin kasashe mawadata, da wanda ake baiwa kasashe masu karamin karfi karkashin shirin COVAX.
Jami’ar ta kara da cewa, rigakafi muhimmin makami ne na yaki da cutar COVID-19, wanda zai taimaka matuka wajen ceto rayukan al’umma, don haka ya kamata a raba shi ga dukkanin sassan duniya, ta yadda bil adama zai amfana da shi.
Daga nan sai ta bayyana kwazon kasar Sin, na shigewa gaba wajen samar da rigakafin ga dukkanin duniya, ta yadda ya zama wata hajar duniya kamar yadda ta alkawarta, yayin da kuma take kara azamar kyautata samuwarsa a farashi mai rahusa ga kasashe masu tasowa.
A daya hannun kuma, Sin ta amsa kiran MDD game da samar da gudummawar rigakafi ga jami’an wanzar da zaman lafiya na sassan duniya daban daban. Hua Ta ce “A shirye muke mu yi hadin gwiwa, da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa wajen samar da rigakafi ga ‘yan wasa, dake shirin shiga a fafata da su yayin gasar wasannin Olympic dake tafe.” (Saminu)

SendShareTweetShare
Previous Post

Shafin Farko: Leadership A Yau Talata 30 Ga Maris 2021

Next Post

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Kira Da Hada Hannu Tsakanin Sin Da Burundi Domin Kiyaye Tsarin Adalci A Duniya

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Shugaban Kasar Sin Ya Yi Kira Da Hada Hannu Tsakanin Sin Da Burundi Domin Kiyaye Tsarin Adalci A Duniya

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Kira Da Hada Hannu Tsakanin Sin Da Burundi Domin Kiyaye Tsarin Adalci A Duniya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version