Sin Na Shirin Harba Kumbon Shenzhou-18 Mai Dauke Da ‘Yan Sama Jannati
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Shirin Harba Kumbon Shenzhou-18 Mai Dauke Da ‘Yan Sama Jannati

byCGTN Hausa
1 year ago
Sin

Yanzu haka shirye shirye sun kammala, na harba kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati, inda ake sa ran harba kumbon a daren gobe Alhamis, da karfe 9 saura minti daya agogon birnin Beijing.

Yayin taron ganawa da manema labarai da ya gudana a Larabar nan, mataimakin daraktan hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Sin ko CMSA Lin Xiqiang, ya ce za a harba kumbon Shenzhou-18 ne daga tashar Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. Kuma zai tashi tare da ‘yan sama jannati uku, Ye Guangfu, da Li Cong da Li Guangsu, karkashin jagorancin Ye.

  • Xi Ya Yi Kira Ga Chongqing Da Ya Rubuta Nasa Tarihi Cikin Aikin Zamanantar Da Kasar Sin
  • Jakadan Sin Dake Amurka: Ana Fatan Amurka Da Sin Su Bi Hanya Daya Don Binciken Yadda Kulla Abota Tsakaninsu

Lin ya kara da cewa, Shenzhou-18 zai kasance kumbo na 32 da kasar Sin za ta harba dauke da ‘yan sama jannati, karkashin shirin ta na binciken samaniya, kana karo na 3 tun bayan kaddamar da matakin aiwatarwa, da bunkasa shirin tashar sararin samaniya kasar.

Jami’in ya ce ‘yan sama jannatin za su kasance cikin falakin kumbon har tsawon kusan watanni 6, kana za su sauko a wurin saukar kumbuna na Dongfeng dake yankin Mongolia ta gida a karshen watan Oktoban bana.

Lin Xiqiang, ya kuma ce tsarin saukar kumbuna na kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, kasancewar kasar na gudanar da karin bincike da bunkasa ayyukan na’urorin fannin kamar yadda aka tsara. Ya kuma ce nan da dan lokaci kadan, za a kammala zaben rukuni na 4 na ‘yan sama jannatin kasar Sin. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Zulum Ya Bukaci Sojojin Nijeriya Da Su Kafa Sansani A Dajin Sambisa

Zulum Ya Bukaci Sojojin Nijeriya Da Su Kafa Sansani A Dajin Sambisa

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version