Sin: Rahoton Neman Asalin Cutar COVID-19 Da Hukumar Leken Asirin Amurka Ta Bayar Na Cike Da Karairayi

Daga CRI HAUSA,

Kwanan baya, ofishin babban darektan leken asirin Amurka ya ba da rahoton neman asalin cutar COVID-19.

Bisa labarin da shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayar a yau Lahadi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya maida martani cewa, wannan rahoto na cike da karairayi, kuma babu gaskiya a cikinsa, kasancewar hukumar ta sha sauya halayyarta sau da dama, a hakika dai rahoto ne na bogi mai cike da siyasa maras tushen kimiyya, ba wanda zai amince da shi.

Wang Wenbin ya nuna cewa, tun watan Agustan bana, wato lokacin da hukumar leken asirin Amurka ta bullo da takaitaccen bayani kan wannan rahoto, Sin ta riga ta bayyana matsayinta na nuna matukar adawa da shi, kuma a cewar malam Bahaushe, karya fure take ba ta ‘ya’ya.

Wang kuma ya jadadda cewa, kamata ya yi Amurka ta daina dora laifi kan wasu, ta mai da hankali kan tinkarar cutar a cikin gidan kasar ta kuma hada kai da sauran kasashe. Wang ya ce, ya kamata Amurka ta dakatar da siyasantar da batun tinkarar cutar COVID-19, da samar da kyakkyawan sharadi ga masana kimiyyar kasa da kasa don su gudanar da bincike kan asalin cutar cikin hadin-gwiwa.

Kamata ya yi Amurka ta dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti da mai da martani kan wasu abubuwan dake jawo hankalin kasa da kasa, har da amincewa da ziyarar masanan WHO cikin kasar, da bude kofar dakin gwajin kwayoyin hallitu na Fort Detrick da sansanin aikin gwajin kwayoyin halittu. (Amina Xu)

Exit mobile version