CRI Hausa" />

Sin Ta Baiwa Kwararrun WHO Cikakkiyar Damar Shiga Ko Ina A Wuhan

Daya daga mambobin tawagar kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO, dake aikin gano asalin cutar COVID-19, ya ce mahukuntan kasar Sin sun baiwa tawagar su cikakkiyar damar shiga ko ina, tare da damar zantawa da dukkanin jami’an da suke bukatar jin ta bakin su, matakin da a cewar sa ya wuce abun da suka zata.

Jami’in dan asalin kasar Birtaniya Peter Daszak, ya ce tawagar su ta mika bukatar ziyartar jerin wurare, da wasu jami’ai da take fatan zantawa da su, kuma ba tare da wata matsala ba gwamnatin Sin ta amince da bukatar su, kamar yadda kafar watsa labarai ta “The Associated Press” ta Amurka ta bayyana.
Bugu da kari, tawagar ta samu zarafin ziyartar asibitocin da suka karbi masu cutar ta COVID-19, lokacin da cutar ta fara bulla tun karshen shekarar 2019 da kuma farkon shekarar 2020.
Irin wannan dama ita ce kuma aka baiwa tawagar, lokacin da ta ziyarci kasuwar kayan abincin ruwa ta Huanan, wadda a nan aka fara samun bullar cutar, suka kuma tattauna da masu sayar da kaya da masu jagorancin kasuwar. (Saminu Alhassan)

Exit mobile version