CRI Hausa" />

Sin Ta Bayar Da Gudunmawar Kayayyakin Kandagarkin COVID-19 Ga Zimbabwe

A ranar Talata kasar Sin ta mika tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Zimbabwe domin taimakawa kasar a yaki da cutar COVID-19.

Kayayyakin sun hada da kayan gwaje gwaje 30,000, wanda gwamnatin kasar Sin ta samar, sai marufin baki da hanci na likitoci guda 220,000, da safar likitoci 40,000, wanda sashen hulda da kasa da kasa na kwamitin tsakiyar jami’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya samar.
Jakadan Sin a kasar Zimbabwe Guo Shaochun, ya mika tallafin ga shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, a bikin da aka shirya a fadar shugaban kasar dake Harare wanda ya samu halartar ministoci da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.
Gudunmawar ta zo ne a daidai lokacin da masu kamuwa da cutar COVID-19 ke ci gaba da karuwa a kasar Zimbabwe. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)

Exit mobile version