Tawagar jami’an lafiyar kasar Sin dake Zimbabwe a ranar Talata sun mika gudunmawar kayayyakin kiwon lafiya ga asibiti mafi girma a kasar Zimbabwe, asibitin na Parirenyatwa Group of Hospitals (PGH), zai samu muhimmiyar damar gudanar da ayyukan yaki da cutuka.
Kayayyakin kiwon lafiyar wadanda hukumar lafiyar kasar Sin ta bayar da gudunmawarsu domin taimakawa kasar yaki da annobar COVID-19.
Kayayyakin sun hada da na’urar taimakawa numfashi, da na’urar dake bibiyar gudanar jini, da na’urar daukar hoton kirji, da injin samar da iskar da ake shaka, da dai sauransu.
Gabanin bayar da gudunmawar, asibitin na PGH ya dogara ne kan wasu injunan gwaje-gwaje na ECG guda biyu, kuma hakan yana tilastawa marasa lafiya biyan makudan kudade ga asibitoci masu zaman kansu don samun lafiya.
Babban jami’i mai kula da asibitin na PGH, Maunganidze ya ce, gwamnatin kasar Sin ta ba da gagarumar gudunmawa ga kasar Zimbabwe a yaki da annobar COVID-19.
Ya ce za su cigaba da tallafa musu da na’urar taimakawa numfashi, daya daga cikin gudunmawar da aka bayar ita ce na’urar da za ta taimakawa numfashi ga marasa lafiya da suka kamu da annobar COVID. Kasancewar annobar COVID-19 ta fi shafar numfashi ne kuma marasa lafiyar dake cikin yanayi mai tsanani suna bukatar na’urar dake taimakawa numfashi, kuma wannan gudunmawa da aka bayar za ta taimaka matuka, in ji jama’in. (Ahmad Fagam)