Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba.
An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan a Japan” Hsieh Chang-ting.
A martanin da ya mayar game da hakan a wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar Guo Jiakun ya ce, kasar Sin tana matukar adawa da matakin gwamnatin Japan na ba da lambar girmamawa ga wadanda ke fafutukar “‘yancin kai na Taiwan” kuma yin hakan wani babban kuskure ne da bangaren Japan ke yunkurin tafkawa kan batun da ya shafi yankin Taiwan na kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














