CRI Hausa" />

Sin Ta Dakatar Da Kafar BBC Daga Yada Shirye Shirye A Cikin Kasar Bisa Karya Dokar Aiki

Hukumar kula da harkokin kafofin watsa labarai ta kasar Sin NRTA, ta dakatar da kafar watsa shirye shirye ta BBC mallakar kasar Birtaniya, daga yada shirye shiryen ta a cikin kasar, bisa laifin karya dokar aiki.

NRTA ta ce BBC ta karya dokokin aikin rediyo da talabijin, da dokoki masu nasaba da harkokin gudanar da shirye shirye kan tauraron dan Adam a ketare masu alaka da kasar ta Sin, wanda hakan ya sabawa sharadin wajibcin labarai ya kasance na gaskiya, da kaucewa son kai. Kaza lika hakan na yin kafar ungulu ga moriyar kasar Sin da ma hadin kan al’ummun ta.
Bisa wadannan dalilai, a cewar hukumar NRTA, kafar BBC ta gaza cimma sharuddan aiwatar da ayyukan ta bisa doka a ketare, don haka, an dakatar da ita daga ci gaba da ayyukan ta a daukacin sassan kasar Sin. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version