Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta shirya tsaf wajen aiwatar da soke haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar jakadanci da kasar ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki.
A yau, wani jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya gabatar da wani batu da ya dace da hakan. Inda ya bayyana cewa, a mataki na gaba, ma’aikatar kasuwanci za ta yi aiki tare da sassan da abin ya shafa, wajen inganta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki don samun ci gaba na bai-daya tare da kasashen Afirka bisa ka’idojin tuntubar juna da samun moriyar juna dai-dai-wa-daida. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)