Sin Ta Fitar Da Tsarin Kaiwa Kololuwar Matsayin Fitar Da Iskar Carbon Kafin Shekarar 2030

Daga CRI Hausa,

Majalissar gudanarwar kasar Sin, ta fitar da cikakken tsarin kaiwa kololuwar matsayin fitar da iskar carbon kafin shekarar 2030.

Tsarin dai na fayyace burin kasar karkashin manufofin ci gaba na shekaru biyar biyar karo na 14, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, da kuma manufofin ci gaba na shekaru biyar biyar karo na 15, wanda za a gudanar tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030, ciki har da batun kara yawan amfani da makamashi da ba ya fitar da iska mai dumama yanayi, da inganta amfani da makamashi, da rage fitar da iskar carbon mai gurbata yanayi baki daya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version