Kwanan baya, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da takardar bayani kan ba da tabbaci ga samar da guraben aikin yi a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta.
Takardar ta yi bayanin cewa, jihar ta maida aikin samar da guraben aiki yi a matsayin wani aiki mai tushe dake tabbatar da zaman rayuwar jama’a, kuma tana kokarin kara karfin ba da horaswa da habaka hanyoyin samun guraben aikin yi, hakan ya sa halin da ake ciki a wannan fanni na samun kyautatuwa, kudin shigar al’umma ya karu sosai.
Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, jihar ta kiyaye hakkin al’umma bisa doka da shari’a don tabbatar da samun guraben aikin yi cikin adalci da kare hakkinsu a fannoni daban-daban.
Dadin dadawa, bayanin ya ce, jihar ta aiwatar da manufofin kasar Sin da ma’aunin kasa da kasa na ‘yan kwadago hakkin bil Adama, don ba da tabbaci ga hakkin samun aikin yi na al’ummun kabilu daban daban a jihar. (Amina Xu)
Dabarun Gwamnatin Sin Ya Baiwa Duniya Kwarin Gwiwar Tinkarar Kalubaloli
“Abin da babba ya hanyo yaro ko ya hau kololuwar...