Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan’adam masu kewayawa kusa da doron duniya, daga cibiyar harba kumbuna ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar.
An harba rukunin taurarin irinsu na tara ne a jiya Lahadi, da misalin karfe 10 da mintuna 15 na dare agogon Beijing, ta amfani da rokar harba kumbuna ta Long March-6 da aka yiwa kwaskwarima. Kuma tuni taurarin suka shiga da’irarsu kamar yadda aka tsara.
Wannan ne karo na 590 da aka yi amfani da rokar Long March wajen gudanar da aikin harba taurarin dan’adam na kasar Sin. (Saminu Alhassan)