Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sin Ta Kakaba Takunkumi Kan Wasu Amurkawa Su 11

Published

on

Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta tabbatar da kakabawa wasu Amurkawa su 11 takunkumi, sakamakon mummunar rawar da suka taka, wajen tsoka baki cikin harkokin yankin HK na kasar Sin, da ma yadda sashen baitulmalin Amurka ya kakaba makamancin wannan takunkumi, kan wasu jami’an hukumomin gwamnatin kasar Sin da na gwamnatin yankin Hong Kong su 11 a ranar 7 ga watan Agustar nan.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin din nan, kakakin ma’aikatar wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ta kakaba takunkumin ne kan wasu Amurkawa, da suka hada da Sanata Marco Rubio, da Ted Cruz, da Josh Hawley, da Tom Cotton, da Pat Toomey, da sauran su, duba da kasancewar su masu hannu dumu dumu a sha’anin tsoma baki cikin batun yankin HK.
A ran 7 ga watan, Amurka dai ta fake da cewa, ta ayyana matakin kakaba takunkumi ga wasu manyan jami’an kasar Sin da na yankin HK ne, sakamakon zargin su da yiwa manufar cin gashin kan yankin Hong Kong kafar ungulu.
To sai dai kuma Mr. Zhao Lijian ya ce, matakan da Amurka ta dauka sun zamo tsoma baki dumu-dumu cikin harkokin yankin HK, da shiga sharo ba shanu cikin harkokin gidan kasar Sin, wanda hakan ya yi matukar keta hurumin dokokin cudanyar kasa da kasa, da ka’idojin alakar kasashen duniya da aka amince da su. Don haka Sin na matukar adawa da matakan na Amurka. (Saminu)
Advertisement

labarai