Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Sin Ta Kakabawa Wasu Mutane Da Kamfanonin Turai Takunkumi

by Sulaiman Ibrahim
March 23, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Sin Ta Kakabawa Wasu Mutane Da Kamfanonin Turai Takunkumi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce kasar ta kakabawa wasu mutane 10, da kamfanonin Turai 4 takunkumi, sakamakon yadda suka yi matukar lahanta moriyar kasar ta Sin, kana suka yada karairayi, da farfaganda maras tushe game da kasar.
Ma’aikatar wajen ta ce, a jiya Talata, kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta kakabawa wasu Sinawa da kamfanonin kasar takunkumi, bisa zargin Sin da keta hakkokin bil Adama a jihar Xinjiang.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin ma’aikatar wajen Sin ya ce matakin EU ya biyo bayan karairayi, da jita jita, da jirkita gaskiya, tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin. Baya ga watsi da kungiyar ke yi da dokokin kasa da kasa da ka’idojin cudanyar kasa da kasa, kungiyar ta gurgunta alakar da ke tsakanin Turai da Sin.
Kakakin ya kara da cewa, wajibi ne EU ta yi watsi da halayyar munafurci, da fuska biyu, tare da dakatar da bin hanya maras bullewa, idan kuwa ba haka ba, Sin za ta ci gaba da maida martani da ya wajaba. (Saminu)

SendShareTweetShare
Previous Post

Xi Jinping Ya Gana Da Masu Yawon Shakatawa A Yayin Ziyararsa A Fujian

Next Post

Wang Yi: Lokacin Yin Amfani Da Karya Don Tsoma Baki Kan Harkokin Cikin Gida Na Kasar Sin Ya Wuce

RelatedPosts

Tsohon Ministan Kudin Girka: Jari Da Sin Ke Zubawa A Afirka Ya Zamo Muhimmin Tallafi Sama Da Mulkin Mallaka Da Kasashen Yamma Suka Yi A Nahiyar

Tsohon Ministan Kudin Girka: Jari Da Sin Ke Zubawa A Afirka Ya Zamo Muhimmin Tallafi Sama Da Mulkin Mallaka Da Kasashen Yamma Suka Yi A Nahiyar

by Sulaiman Ibrahim
6 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon ministan kudin kasar Girka Yanis Varoufakis,...

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19

by Sulaiman Ibrahim
8 hours ago
0

Daga Fa’iza Mustapha Har yanzu duniya na ci gaba da...

Manufar Wariyar Launin Fata Ta Amurka Na Keta Hakkin Dan Adam

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Daga CRI Hausa A shekarar 1962, marubucin kasar Amurka, ‘dan...

Next Post
Wang Yi: Lokacin Yin Amfani Da Karya Don Tsoma Baki Kan Harkokin Cikin Gida Na Kasar Sin Ya Wuce

Wang Yi: Lokacin Yin Amfani Da Karya Don Tsoma Baki Kan Harkokin Cikin Gida Na Kasar Sin Ya Wuce

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version