Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dakatar Da Tsoma Baki Kan Harkokin Cikin Gida Na Sin Ta Hanyar Yin Amfani Da Batun Hakkin Dan Adam

Game da abubuwan dake shafar kasar Sin a cikin rahoton hakkin dan Adam na kasa da kasa na shekarar 2018 da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gabatar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a jiya Alhamis cewa, Sin ta ki amincewa da wannan batu ba, ta kuma kalubalanci kasar Amurka da ta nuna daidaita ga yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin da dakatar da tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin.

Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, abubuwan dake shafar kasar Sin a cikin rahoton kasar Amurka sun yi daidai da na shekarun da suka gabata, wadanda suka nuna rashin daidaici da rashin gaskiya da zargi kasar Sin ba tare da tushe ba. Ya ce Sin ta ki amincewa da hakan, kana ta riga ta tuntubi kasar Amurka a hukunce don daidaita wannan batu. (Mai Fassara: Zainab)

Exit mobile version