Sin Ta Kare Ingancin Rigakafin Da Take Samarwa Domin Amfanin Sassan Duniya

Daga CRI Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce sama da shugabannin kasashen duniya 30 ne suka karbi rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da Sin ta samar, bayan da aka amince da amfani da su a matakin gaggawa a akalla kasashen duniya 100.

Zhao na wannan tsokaci yayin da yake martani ga wasu rahotanni, na wasu kafafen watsa labarai, wadanda a baya bayan nan ke nuna shakku game da inganci da nagartar rigakafin da ake sarrafawa a kasar Sin.

Jami’in ya kuma jaddada matsayin kasar Sin, ta ci gaba da yin hadin gwiwa da sassan kasa da kasa, a fannin samar da rigakafin wannan cuta, yana mai cewa kawo yanzu, kasar Sin ta samar da rigakafin COVID-19 miliyan 500 ga sama da kasashen duniya da hukumomi 100, yayin da kuma take shirin samarwa shirin COVAX, na hukumar lafiya ta duniya WHO rigakafin cutar har miliyan 110, cikin watanni 4 masu zuwa.

Tuni dai WHO ta amince da amfani da rigakafin da kamfanonin Sinovac da Sinopharm suke samarwa a mataki na gaggawa. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hasua)

Exit mobile version