Sin Ta Ki Amincewa Da Dora Wa Wasu Laifi Ta Hanyar Siyasantar Da Binciken Asalin Cutar COVID-19

Daga CRI Hausa,

Mataimakin shugaban hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Zeng Yixin ya bayyanawa ‘yan jarida game da rahoton aikin binciken asalin cutar COVID-19 wanda hukumar leken asirin Amurka ta gabatar cewa, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ba hukumar ilmin likitanci ba ce, amma ta gabatar da rahoton binciken asalin cutar COVID-19, hakan ya bayyana a fili za a gano wanda ya siyasantar da batun gano asalin cutar. Aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 batu ne na kimiyya, gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan yin wannan aiki tun daga lokacin farko na bullar cutar a kasar, da kin amincewa da siyasantar da aikin, da kuma kaucewa dora alhaki kan wasu kasashe.

Zeng Yixin ya jaddada cewa, aikin binciken asalin kwayar cutar aiki ne na kimiyya mai sarkakkiya, ya kamata masanan kimiyya na duniya su yi hadin gwiwa don yin aikin.

Yana fatan Amurka za ta fahimci cewa, kwayar cutar, abokiyar gaba ce ga dukkan bil Adama, ta maida aikin neman asalin kwayar cutar a matsayin aikin kimiyya, da sa kaimi ga masanan kimiyya na duniya ciki har da na kasar Amurka da su yi hadin gwiwa tare don kara yin nazari kan aikin. (Zainab)

Exit mobile version