CRI Hausa" />

Sin Ta Nemi Kasar Amurka Ta Yi Bayani Kan Harin Da Hukumar CIA Ta Sha Kai Wa Yanar Gizo Ta Sin

Kamfanin 360 na kasar Sin, ya gano cewa hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato CIA, ta sha kai hare-hare ta yanar gizo ga Sin. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a ranar 4 ga wata, cewar Sin ta kalubalanci Amurka, da ta yi bayani game da batun, da dakatar da wannan aiki nan take.
Zhao Lijian ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka, da hukumomin da abin ya shafa, sun sabawa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da leken asiri, da sa ido, da kai hari ta yanar gizo ga gwamnatoci, da kamfanoni, da kuma mutanen sauran kasashen duniya, inda kasar Amurka ta kasance mafi yawan kai hari ta yanar gizo ga sauran kasashen duniya. Amma kasar Amurka ta kan mai da ita kanta a matsayin kasar dake tinkarar harin yanar gizo a kullum, hakan ya shaida cewa, kasar Amurka ta dauki ma’auni biyu kan batun.
Zhao Lijian ya jaddada cewa, Sin ta sha hare-haren da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta kan kai wa yanar gizo nata. Kaza lika Sin ta taba tuntubar Amurka game da lamarin. Kana ta sake kalubalantar kasar Amurka, da ta yi bayani game da lamarin, da dakatar da hakan cikin gaggawa, da kuma mayar wa kasar Sin, da sauran kasashen duniya wani yanayin zaman lafiya, da bude kofa, da hadin gwiwa a shafukan intanet. (Mai Fassarawa: Zainab Zhang)

Exit mobile version