Sin Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Kara Haraji Kan Karafa Da Gorar Ruwa Dake Shiga Kasar Daga Kasar Sin
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Kara Haraji Kan Karafa Da Gorar Ruwa Dake Shiga Kasar Daga Kasar Sin

byCGTN Hausa
1 year ago
Sin

Dangane da barazanar da Amurka ta yi na kara haraji kan karafa da gorar ruwa da ke shiga kasar daga kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a, a gun taron manema labaru da aka saba yi cewa, matakin na Amurka ya illata dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da Sin, kuma ya sabawa ra’ayin bai daya da aka cimma a yayin tattaunawar shugabannin kasashen biyu da aka yi a birnin San Francisco.

Kakakin ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka da ta shude ta kara haraji kan karafa da gorar ruwa na wasu mambobin kungiyar cinikayya ta WTO bisa hujjar wai “tsaron kasa”, wanda kungiyar ta riga ta yanke hukunci cewa, matakin ya karya ka’idojinta. Amurka ba gaza gyara kuskurenta kadai ta yi ba, har ma tana barazanar kara haraji tare da sanar da kaddamar da wani sabon bincike bisa ayar doka ta 301, wanda ke kara yin kuskure. Ya ce kasar Sin za ta sa ido sosai kan yadda binciken ke gudana, tare da daukar dukkan matakan da suka dace don kare hakki da muradunta.

A yayin da yake ba da amsa kan kara wa batun “wuce gona da iri wajen samar da hajoji a Sin” gishiri da Amurka ta yi a baya-bayan nan, kakakin ya bayyana cewa, abin da ake kira “ra’ayin wuce gona da iri wajen samar da hajoji a kasar Sin” da Amurka ta gabatar, tamkar wani batu ne da ya danganci tattalin arziki, amma hakika mugun nufin kasar ne na murkushe ci gaban masana’antun kasar Sin, da nufin neman wani matsayi mafi dacewa na yin takara da samun fifiko a kasuwa, wanda ya kasance wani mataki na cin zali da matsawa kasar Sin ta fuskar tattalin arziki a bayyane. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
An Kunna Wutar Fara Gasar Olympics A Kasar Girka

An Kunna Wutar Fara Gasar Olympics A Kasar Girka

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version