Connect with us

RAHOTANNI

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Kan Nuna Karfin Tuwo Ga Sinawa ‘Yan Yawon Shakatawa Da Sweden Ta Yi

Published

on

A yau Asabar 15 ga wata, ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden, ya bayar da sanarwa game da batun ’yan sandan Sweden, wadanda suka nuna karfin tuwo kan masu yawon shakatawa Sinawa 3, lamarin da ya faru da sanyin safiyar ranar 2 ga wata, inda ya bayyana matukar kaduwa da jin aukuwar wannan lamarin, sa’anan ya yi tir da abin da ’yan sandan suka yi.

Zhang Lei, dan karamin jakadan Sin da ke Sweden ya bayyana cewa, ofishin jakadancin da ma’aikatar harkokin wajen Sin, sun riga sun nuna rashin jin dadinsu ga gwamnatin Sweden daya bayan daya, inda suka jaddada cewa, abin da ’yan sandan suka yi ya keta hakkin dan Adam ne, ya kuma kawo illa ga tsaron ’yan kasar Sin, kana ya bukaci gwamnatin kasar Sweden da ta yi bincike kan batun cikin hanzari, da amsa bukatun masu yawon shakatawar na yanke hukunci ga ’yan sandan, da neman gafara gare su, da kuma biyansu kudin diyya. Bugu da kari, ofishin bai fahimci mene ne dalilin da ya sa bangaren Sweden bai mayar da martani kan batun ba, kuma ya sake bukatar bangaren Sweden da ya dauki matakai nan da nan, don tabbatar da tsaro da hakkin Sinawa da ke Sweden bisa doka.

An labarta cewa, da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Satumba, Mista Zeng da iyayensa daga kasar Sin sun isa wani otel dake birnin Stockholm. Sabo da lokacin yin rajistar dakinsu bai yi ba, Mista Zeng ya bukaci biyan kudi ga otel din don neman baiwa iyayensa damar su huta a kujerar dake babban dakin karbar baki na otel din, inda ya ce shekarun haihuwa na iyayensa sun zarce 60 don haka suna da bukatar hutawa. Amma bangaren otel din bai amince ba, har ma ya kira ’yan sanda domin daidaita batun. Da isowar ’yan sanda otel din, sai sun janyo Mista Zeng da iyayensa daga otel ta hanyar nuna karfin tuwo, suka kai su zuwa wani filin kaburbura dake da kilomita fiye da goma da birnin Stockholm, suka ajiye su a can. Ba yadda za su yi, sai Mista Zeng da iyayensa suka nemi taimako daga wajen mutane, sa’an nan suka samu damar komawa birnin Stockholm. Daga baya kuma sun tuntubi ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden. (Kande Gao, ma’aikatan Sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: