Kasar Sin ta fitar da manyan manhajojin AI har 1,509, matakin da ya sanya ta kaiwa matsayi na daya cikin jerin sassan duniya da suka fitar da jimillar irin wadannan manhajoji 3,755. Masana na ganin bunkasar sashen masana’antun fasahohin AI na kasar Sin zai ingiza sabbin nasarori a fannin.
A jiya Lahadi, yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa game da AI na shekarar 2025, an gudanar da baje kolin nasarori da aka cimma a fannin masana’antun AI na Sin. Kuma a cewar sashen lura da bayanai na cibiyar bincike game da harkokin sadarwa ta Sin, adadin kamfanonin AI na sassa daban daban na duniya ya kai sama da 35,000, yayin da Sin ke da irin wadannan kamfanoni har 5,100, adadin da ya kai kaso 15 bisa dari na jimillar wanda ake da shi a duniya baki daya.
Rahotanni na cewa, adadin masana’antun fannin na ta karuwa ta fuskar kayayyakin more rayuwa, da kayayyakin da yake samarwa domin amfani a masana’antu. Kazalika, akwai jimillar kamfanonin AI masu daraja da yawansu ya kai 271 a duniya baki daya, ciki har da 71 na kasar Sin, adadin da ya kai kaso 26 bisa dari na jimillar wadanda ake da su a duniya. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)