A shekarar 2024 da ta gabata, kamfanonin kasar Sin da masu bincike na kasar, sun gabatar da sabbin bukatun neman ikon mallakar fasaha har 20,081 ga ofishin rajistar ikon mallakar fasaha na Turai ko EPO, kamar dai yadda alkaluman shekarar 2024 da ofishin ya fitar a yau Talata suka nuna.
Wannan adadi ya kai kaso 10.1 bisa dari na jimillar neman izini da ofishin na EPO ya karba a bara, wanda hakan ya tabbatar da Sin a matsayi na 4 cikin jerin kasashe mafiya gabatar da bukatar ga ofishin a duniya baki daya.
A jerin kamfanoni dake cikin jadawalin na EPO, kamfanin Huawei na Sin na matsayi na biyu, da bukatun neman ikon mallakar fasaha har 4,322. Baya ga Huawei, akwai kuma wasu kamfanonin Sin 5 da su ma ke cikin kamfanoni 50 na sahun farko a jadawalin, wanda hakan ke nuni ga yadda Sin ke samun karin tagomashi a fannin kirkire-kirkire, da shiga a dama da ita wajen neman ikon mallakar fasahohi a Turai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)