CRI Hausa" />

Sin Ta Sanya Takunkumi Kan Amurkawa 28 Ciki Har Da Pompeo

Kasar Sin ta sanya takunkumi kan wasu Amurkawa 28 wadanda take tuhuma da laifin karya dokokin ikon kasar, kuma su ne ke da alhakin laifuffuka da dama da Amurka ta aikata ga kasar Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar da hakan a yau Alhamis.

Mutanen sun hada da Michael R. Pompeo, Peter K. Navarro, Robert C. O’Brien, David R. Stilwell, Matthew Pottinger, Alex M. Azar II, Keith J. Krach, da kuma Kelly D. K. mai karfin fada a ji a gwamnatin Trump, sannan akwai John R. Bolton da Stephen K. Bannon.
A ‘yan shekarun da suka gabata, masu adawa da manufofin siyasar kasar Sin dake Amurka, saboda biyan bukatun siyasa na kashin kansu, da rashin adalci, gami da nuna kiyayya ga kasar Sin, da kuma rashin kaunar da suke yiwa moriyar mutanen Sin da Amurka, sun kulla makirci, sun kuma kaddamar da munanan kudurori gami da yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda ya lahanta moriyar kasar Sin, ya bakanta ran Sinawa, kuma ya yi mummunar illa da haifar da koma baya ga dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar.
Kakakin ya ce, gwamnatin Sin a shirye take ta kare matsayin ikon kasarta, da tsaron kasar, gami da ci gaban moriyarta.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version