Rahotanni daga jaridar “The New York Times”, na cewa mahukuntan Sin na shirin yiwa ’yan kasar miliyan 50 allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, daga nan zuwa ran 15 ga watan Fabarairu, lokacin da za a yi bukukuwan sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, lokaci da miliyoyin al’ummar kasar ke yin tafiye-tafiye.
Jaridar ta rawaito wani kwararre a fannin rigakafin Tao Lina, na cewa hukumar lafiyar Sin, ta bayyana wannan shiri ne yayin wani taro ta kafar bidiyo da jami’an lardunan kasar a ranar 15 ga watan nan.
Tao Lina, wanda ke aiki a birnin Shanghai, kuma babban jami’in ayyukan rigakafi a cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta kasar, ya ce an kiyasta adadin mutane miliyan 50 din ne, daga adadin mutanen da ake hasashen za su fi bukatar rigakafin a karon farko.
Jami’in ya ce lardunan kasar Sin, na ci gaba da lasafta adadin mutanen su. A kuma wannan wata, gwamnati ta ce za a ba da fifiko, wajen gudanar da rigakafin ga kwararru dake aikin kula da lafiyar al’umma, da matukan jiragen sama, da masu aiki a wuraren sayar da abinci, da kuma sauran mutane dake cikin hadarin harbuwa da cutar cikin sauri. (Saminu Hassan)