Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta taya Ngozi Okonjo-Iweala daga tarayyar Najeriya, murnar zama sabuwar babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce Okonjo-Iweala, ta taka rawar gani wajen tallafawa ayyukan yaki da fatara a kasashe masu tasowa, ta kuma yi ayyuka masu nasaba da bunkasa rigakafi da na kiwon lafiya, tana kuma da kwarewar jagoranci, a harkokin gudanar da hukumomin kasa da kasa. Sanarwar ta kara da cewa, nadin na ta, ya dace da hasashen dukkanin sassa.
Kaza lika sanarwar ta ce, duk da annobar COVID-19 da kalubalen da tsarin cinikayyar duniya ke fuskanta, Sin na da cikakken karfin gwiwar cewa, Okonjo-Iweala za ta cimma nasarar sauke nauyin jagorancin kungiyar WTO, tare da taka rawar gani wajen aiwatar da matakan hadin gwiwar yaki da COVID-19, da farfado da tattalin arzikin duniya.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, a matsayin ta na kasa mai tasowa mai sauke nauyin dake wuyanta, kasar Sin na goyon bayan tsarin cudanyar cinikayyar duniya, za ta kuma taka muhimmiyar rawa a ayyukan WTO, da gyaran fuskar da ake fatan yiwa kungiyar, za ta kuma yi aiki tare da sabuwar babbar daraktar kungiyar, ta yadda hakan zai taimakawa WTOn aiwatar da gudummawar da za ta inganta jagorancin duniya, da kare moriyar al’ummun sassan duniyar daban daban. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)