Sin Ta Yi Kira Ga Sakatariyar MDD Da Ta Ci Gaba Da Karfafa Fannin Kasafin Kudi Na Kiyaye Zaman Lafiya
  • English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Yi Kira Ga Sakatariyar MDD Da Ta Ci Gaba Da Karfafa Fannin Kasafin Kudi Na Kiyaye Zaman Lafiya

byCMG Hausa
2 years ago
MDD

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga sakatariyar MDD da ta ci gaba da karfafa cikakken tsarin gudanar da ayyukan kasafin kudi na wanzar da zaman lafiya, da karfafa tsarin kula da harkokin cikin gida yadda ya kamata, da inganta ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin jawabinsa a wajen bude taro karo na biyu na kwamitin gudanarwa da kasafin kudi na kwamiti na biyar, na babban taron MDD karo na 77, wanda ya gudana a wannan rana.

  • Ding Liren Ya Yi Nasara Kan Nepomniachtchi Inda Ya Zamo Basine Dan Wasan Dara Na Farko Da Ya Lashe Gasar Duniya

A cewar sa, kudi shi ne tushe, kuma muhimmin ginshikin gudanar da harkokin MDD. Kuma a matsayin kasafin kudi mafi girma na MDD, kudaden wanzar da zaman lafiya sun kai biliyoyin daloli. Don haka a ko da yaushe, kasar Sin ke kira ga kwamitin na biyar na babban taron MDD, da ya yi nazari sosai kan kasafin kudin kiyaye zaman lafiya, bisa ka’idojin kimiyya da lura, da samar da albarkatun da suka dace don gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin binciken kudi ya gudanar da aikin sa ido sosai, da ba da shawarwari masu ma’ana, da kuma ci gaba da inganta tsarin tafiyar da kasafin kudi.

Kaza lika kasar Sin tana kuma goyon bayan MDD, wajen cika hakkinta na biyan diyya ga kasashen da ke ba da gudummawar sojoji da ‘yan sanda cikin sauri.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu
Daga Birnin Sin

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Next Post
Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni

Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni

LABARAI MASU NASABA

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version