Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Sun Weidong ya gana da jakadan Japan a Sin Kishi Nobuo bisa umurnin gwamnatin kasar a jiya Alhamis, inda ya yi tsokaci a hukumance kan kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da kasar Sin.
Sun ya ce, batun Taiwan na da matukar muhimmanci cikin muradun Sin, kuma ba za a iya tauye shi ba. Taiwan yanki ne na Sin, kuma harkokin Taiwan batu ne na cikin gidan Sin. Tsara yadda za a warware matsalar Taiwan aiki ne na kasar Sin, kuma ba za a yi katsalandan a kai ba. Bana ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sin ta yi da mamayar dakarun Japan da kuma yakin duniya na biyu na kin tafarkin murdiyya, da kuma cika shekaru 80 da fitar yankin Taiwan daga mulkin mallakar Japan tare da dawo da shi karkashin Sin.
Ya kara da cewa, a shekaru 80 da suka gabata, jaruman jama’ar Sin sun yi yaki na tsawon shekaru 14 domin nuna turjiya ga maharan Japan. A yau, duk wanda ya yi yunkurin katsalandan a harkokin dunkulewar Sin, ko shakka babu Sin za ta mayar da martani mai tsanani!
Sun ya kuma bukaci Japan da ta yi tunani mai zurfi game da laifuffukanta na tarihi, ta daidaita kura-kuranta, kuma ta janye kalamanta marasa kyau, kuma ta dakatar da tafiya a kan hanyar da ba ta dace ba. In ba haka ba, Japan za ta dauki alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya, kuma tabbas kaikayi zai koma kan mashekiya! (Amina Xu)













