Daga Ahmad Fagam
Ilmi shi ne jigon rayuwa, kuma kamar yadda ’yan magana kan ce, “ilmi gishirin zaman duniya.” Ko shakka babu, ilmi shine kashin bayan cigaban kowace al’umma, shine fitilar dake haskakawa alumma hanya domin samun makoma mai haske daga dukkan fannoni. Hakika, duba da irin kwararan matakan da gwamnatin Sin ke dauka wajen bunkasawa da kuma kyautata cigaban ilmi a kasar ya kasance wani muhimmin al’amari ga kasar. Koda yake, dama dai masu hikimar Magana na cewa, “da sanyin safe ake kama fara.” Bisa yadda mahukuntan kasar suka yi farar dabara wajen zuba matukan kudade a fannin bunkasa ilmi tun daga tushe da kuma irin tagomashin da ake baiwa wannan muhimmin bangare sun taimaka wajen cimma nasarar kaiwa matakin da kasar take kai a halin yanzu. Alal misali, kamar yadda ma’aikatar kudin kasar ta sanar a karshen wannan mako cewa gwamnatin Sin ta kashe kudi kimanin yuan biliyan 931.6 (kwatankwacin dala biliyan 143.7) domin daga matsayin daidaiton ci gaban aikin ba da ilmin kasar karkashin shirinta na raya kasa na shekaru 5 karo na 13 tsakanin shekarar 2016-2020. Sannan kasar ta ware kudin da ya kai yuan biliyan 587.7 karkashin shirin samar da tabbaci na bunkasa ilmin birane da na karkara a cikin shekaru biyar din da suka gabata. A shekarar 2020, kimanin dalibai miliyan 154 ne aka yafewa biyan kudin makaranta da na sauran hidimomi karkashin shirin samar da ilmi na wajibi, kana daga cikin adadin, dalibai miliyan 25 da suka fito daga iyalai marasa galihi, an samar musu da tallafin saukaka musu zaman rayuwa. Daga shekarar 2016 zuwa 2020, an kashe kimanin yuan biliyan 163.9 domin inganta yanayin makarantu a yankunan al’ummu masu karamin karfi. A cikin wannan wa’adi, gwamnati ta kashe kudade kimanin yuan biliyan 103 karkashin wani shirin bayar da tallafi na gwaji, da nufin samar da abinci mai gina jiki ga yara kanana daga yankuna masu fama da talauci. Ko shakka babu, wadannan matakai da makamantansu sun yi matukar taka rawar gani wajen tabbatar da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin bunkasa cigaba ilmi. (Ahmad Fagam)