Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Sin Tana Kara Cimma Manyan Nasarori A Fannin Binciken Sararin Samaniya

by
1 year ago
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Sin Tana Kara Cimma Manyan Nasarori A Fannin Binciken Sararin Samaniya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A ranar Laraba 10 ga watan Faburairun nan ne, naurar binciken duniyar Mars mai lakabin Tianwen-1 kirar kasar Sin, ta cimma nasarar shiga falakin duniyar Mars, wanda hakan ya kasance karon farko da kasar Sin ta kai ga nasarar shigar da wani kumbon bincikenta cikin wannan Jar Duniya kamar dai yadda ake yiwa duniyar Mars din lakabi da haka.

Masu aikin lura, tare da sarrafa wannan naura, sun ce ta kai ga shiga falakinta a duniyar ta Mars ne da karfe 8 saura mintuna 8 na almuru, bayan haye kalubale daban daban na fasaha.
Tianwen-1 ya zamo aikin sarrafa kumbuna, da naurori daban daban da kasar Sin ta aiwatar cikin gwamman shekaru, yayin da kasar ke kara fadada ci gabanta a fannin binciken kimiyya da fasaha, da ayyukan sararin samaniya da na ’yan sama jannati.
A karo da dama, Sin ta sha harba kumbunan binciken samaniya masu dauke da ’yan sama jannati, da wadanda ke aiki ba tare da ’yan sama jannati ba.
Ana iya cewa, aikin da Tianwen-1 zai yi a duniyar Mars, zai zamo kari kan manyan nasarorin da Sin ta samu a wannan fanni na nazarin duniyoyin da ba na bil Adama ba. Wato kari kan aikace-aikace da aka cimma nasararsu, kamar na jerin kumbuna Beidou masu aikin samar da hidimar taswira, wanda kasar Sin ta fara cikin shekara ta 2000, ana kuma kammala harba rukunin taurarinsa a bara.
Kaza lika, aikin ya dada tabbatar da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin amfani da rukunin rokar Long March, da aka rika amfani da su wajen harba taurarin bil Adama, da kumbuna, da sauran naurorin binciken sararin samaniya.
Ko shakka babu, naurar Tianwen-1, ta kafa tarihin zama irinta ta farko da kasar Sin ta harba, musamman domin binciken duniyar Mars, bayan harba ta daga tashar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan a ranar 23 ta Yulin bara. Aikin da tuni ya kafa harsashin ci gaban kasar Sin, a fannin binciken duniyoyi daban daban baya ga duniyar bil Adama. (Saminu Alhassan)

Labarai Masu Nasaba

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande Ya Rasu

Next Post

Uwargidan Shugaban Sin Ta Tura Wasika Zuwa Makarantar Burg Gymnasium Ta Jamus

Labarai Masu Nasaba

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

by
15 hours ago
0

...

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

by CMG Hausa
15 hours ago
0

...

Jakadan Sin Ya Yi Kira A Bada Fifiko Wajen Bunkasa Ci Gaban Yankin Sahel

Jakadan Sin Ya Yi Kira A Bada Fifiko Wajen Bunkasa Ci Gaban Yankin Sahel

by Abdulrazaq Yahuza Jere
15 hours ago
0

...

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin Kungiyar BRICS

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin Kungiyar BRICS

by CMG Hausa
16 hours ago
0

...

Next Post
Uwargidan Shugaban Sin Ta Tura Wasika Zuwa Makarantar Burg Gymnasium Ta Jamus

Uwargidan Shugaban Sin Ta Tura Wasika Zuwa Makarantar Burg Gymnasium Ta Jamus

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Loading Comments...
 
    %d bloggers like this: