Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar

byCMG Hausa
2 years ago
FILE - The logo of the United Nations Educational, Scientific and Cultural Organisation (UNESCO) is seen during the 39th session of the General Conference at the UNESCO headquarters, Oct.31 2017 in Paris. The United States is ready to rejoin the U.N. cultural and scientific agency UNESCO – and pay more than $600 million in back dues -- after a decade-long dispute sparked by the organization's move to include Palestine as a member. (AP Photo/Francois Mori, File)

Jiya Juma’a 30 ga watan Yuni, an zartas da wani daftarin kuduri yayin taron musamman na babban taron UNESCO wato hukumar kula da ba da ilmi da kimiyya da al’ada ta MDD, inda aka amince da maido da matsayin mambar kasar Amurka a hukumar tun daga watan Yulin da ake ciki daga duk fannoni.

Daga baya zaunannen wakilin kasar Sin dake hukumar Yang Jin ya jaddada cewa, bayan dawowar Amurka hukumar, ya dace ta yi kokari domin ingiza hada kan hukumar, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin hukumar, a maimakon raba kai ko kawo baraka.

  • Sin Ta Yi Kira Da A Samar Da Yanayin Shawo Kan Rikicin Ukraine Baki Daya

Yang Jin ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarin da ta dauka, ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, kuma ta biya kudin haraji a kan lokaci, tare kuma da biyar daukacin kudin haraji da ba ta biya a cikin ‘yan shekarun da suka gabata ba a kan lokaci.

Bisa kudurin da aka zartas da shi, Amurka za ta biya kudin haraji da hukumar take binta a kai a kai, a sa’i daya kuma, za ta samar da tallafin kudi ga hukumar domin gudanar da ayyukan dake shafar tsaron lafiyar manema labarai da ba da ilmi a kasashen Afirka.

Rahotannin da kafofin watsa labarai suka gabatar sun nuna cewa, gaba daya adadin kudin da hukumar UNESCO take binta ya riga ya kai dalar Amurka miliyan 619.

An labarta cewa, Amurka ta taba janye jiki daga hukumar sau biyu wato a shekarar 1984 da kuma ta 2018, lamarin da ya gamu da suka daga kasa da kasa. (Mai fassara: Jamila)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Next Post
Sarkin Noman Gaya Ya Nemi Gwamna Abba Ya Bullo Da Sabon Tsarin Bunkasa Noma

Sarkin Noman Gaya Ya Nemi Gwamna Abba Ya Bullo Da Sabon Tsarin Bunkasa Noma

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version