Sin: Yin Katsa-landan Da Sanya Takunkumin Kashin Kai Ba Za Su Warware Batun Tsakiyar Afirka Ba
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Yin Katsa-landan Da Sanya Takunkumin Kashin Kai Ba Za Su Warware Batun Tsakiyar Afirka Ba

byCMG Hausa
2 years ago
Sin

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya jaddada jiya Litinin cewa, yin katsa-landan da sanya takunkumin kashin kai, ba za su warware batun tsakiyar Afirka ba.

A yayin muhawarar da kwamitin sulhu ya shirya kan batun tsakiyar Afirka, Dai Bing ya ce, abubuwan da suka faru a wasu kasashen Afirka sun nuna cewa, wajibi ne a dogara da karfin kasashen nahiyar wajen daidaita batun Afirka.

  • Qin Gang Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministan Harkokin Wajen Afirka Ta Kudu

Kana wajibi ne kasashen duniya su mutunta ikon mulkin kan kasashen Afirka, da ikonsu na daidaita batun, a kokarin samar da kyakkyawan karsashi na kiyaye kwanciyar hankali ta fuskar siyasa a yankin.

Ya ce kasar Sin na da imanin cewa, ya kamata kasashen duniya su gudanar da bincike kan ayyukan kiyaye hakkin dan Adam bisa sanin ya kamata, da hakikanin halin da kasashe masu ruwa da tsaki suke ciki, da kuma bukatun jama’arsu, su kuma kauce wa kiyaye hakkin dan Adam a fatar baka kawai, kuma kar su yi amfani da batun kare hakkin dan Adam domin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.

Jakadan na kasar Sin ya kara da cewa, yadda wasu muhimman rukunonin tattalin arziki suka aiwatar da manufofin hada-hadar kudi da ba su dace ba, da tura barazanar tattalin arziki da matsalolin kudi da suke fama da su kan wasu kasashe, da satar dukiyoyin kasashe masu tasowa, barazana ce mafi muni ga kasashen Afirka masu tasowa.

Don haka dole ne kasashe masu sukuni, da hukumomin kudi na kasa da kasa, su fahimci matsalolin da kasashen da ke yankin suke fama da su, su cika alkawarin bayar da tallafin raya kasa, da kiyaye zuba kudaden jin kai, a kokarin taimakawa wadannan kasashe jure wahalhalu. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Sin Ta Bude Ofishin Jakadanci S Kasar Honduras

Sin Ta Bude Ofishin Jakadanci S Kasar Honduras

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version