Sin Za Ta Ci Gaba Da Aiki Tare Da Sauran Sassa Wajen Kare Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce a matsayin ta na mambar dindindin a kwamitin tsaron MDD, kuma kasa dake da adadi mafi yawa na dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a sassan duniya, cikin kasashe 5 masu matsayin dindindin a majalisar, Sin za ta ci gaba da aiki tare da sauran sassan masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da kare lafiyar dakarun wanzar da zaman lafiya.

Zhao wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya kuma tabo batun alakar Sin da Rasha, inda ya ce a shirye kasar Sin take, ta yi aiki kafada da kafada da Rasha da sauran kasashen duniya, wajen tallafawa, da aiwatar da matakan cudanyar dukkanin bangarori, tare da bunkasawa, da kuma sanya salon dimokaradiyya cikin alakar kasa da kasa.

Game da hadin gwiwar rigakafin cutar COVID-19 kuwa, jami’in ya ce tsibirin Solomon ne kasar farko, da daukacin al’ummar ta suka karbi rigakafin kasar Sin, wanda hakan ke nuni ga cikakken burin Sin na cika alkawarin da ta yi, na mayar da rigakafin da ta sarrafa, hajar daukacin bil adama. Zhao Lijian ya kuma bayyana cewa, Sin na maraba da aniyar kasar Iran, ta cimma matsaya tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, a fannin tsawaita hadin gwiwa. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version