Daga CRI Hausa
Kasar Sin ta kammala wani nazari a mataki na hudu karkashin shirinta na binciken duniyar wata, kana kasar tana sa ran gina wata tashar binciken duniyar wata ta kasa da kasa a kudancin gefen duniyar wata nan wani dan lokaci mai zuwa, Wu Weiren, babban jagoran shirin binciken duniyar wata na kasar Sin ya bayyana hakan.
A wata tattaunawar da ya yi da kafar yada labaran aikin binciken sararin samaniyar kasar Sin wato China Space News, Wu ya bayyana cewa, za a gudanar da ayyuka guda uku a mataki na hudu na shirin binciken duniyar watan. Wadanda suka hada da karbar samfura daga shiyyar kudancin gefen duniyar wata da na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6, da gudanar da binciken kwakwaf a kudancin gefen duniyar wata ta hanyar yin amfani da na’urar bincike ta Chang’e-7, da kuma yin wasu muhimman gwaje-gwajen fasahohi domin gina tashar binciken duniyar wata ta hanyar yin amfani da na’urar bincike ta Chang’e-8.
Mista Wu ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne a samu wani yanani a lokutan dare da rana a kudancin gefen duniyar watan, kamar yanayin da ya yi daidai da na yankin arewaci da kudancin duniyar da muke ciki. Yanayin juyawar wata zai iya yin daidai da fitowarsa da komawarsa, wanda dukkansu a cikin kwanaki 28 ne. Sannan kuma, akwai yiwuwar shafe sama da kwanaki 180 a jere ana samun yanayi mai haske a kudancin gefen duniyar wata, wanda zai kasancewa yanayi mafi dacewa ga masu gudanar da ayyukan binciken kimiyya a duniyar watan.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)