Kasar Sin ta fitar da wata ka’idar kafa shirin samar da masu tsaron dazuka a fadin kasar, a ci gaba da kokarin da take na kare dazuka da yankunan ciyayi.
Ofisoshin kwamitin tsakiya na JKS da na majalisar gudanarwar kasar ne suka fitar da shirin wanda za a kaddamar a fadin kasar a watan Yunin 2022.
Bisa ka’idar, za a nada masu tsaron dazuka a dukkan matakan larduna. Ta kuma fayyace hakkokin da suka rataya a wuyansu na kare albarkatun dazuka da na yankunan ciyayi.
Karkashin shirin, Sin za ta karfafa kare muhalli da farfado da dazuka da yankunan ciyayi da inganta shuka bishiyoyi masu yawa da bunkasa bibiya da sa ido kan albarkatun dazuka da yankunan ciyayi ta hanyar amfani da fasahohin zamani.
Za kuma a karfafa ayyukan kandagarki da tunkarar kwari masu hadari da cututtukan tsirrai da kuma annoba kamar gobara. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)