Na’urar bincken duniyar wata ta Chang’e-5 da kasar Sin ta harba zuwa duniyar wata, ta cimma nasara a aikin binciken duniyar wata na kasar mai zurfi, inda ta samar da abubuwa guda biyar a karon farko, ciki har da tattarowa da dawo da samfura, da dawo daga duniyar wata, da shiga falaki, matakin da ya aza wani tubali a aikin binciken sararin samaniya a nan gaba.
Mataimakin shugaban hukumar binciken sararin samaniyan kasar Sin Wu Yanhua, shi ne ya bayyana haka Alhamis din nan, lokacin da ya ke gabatar da shirin na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ga taron manema labarai, yana mai cewa, kasar Sin ta yi aiki da Turai da kasashen Namibia, da Argentina, da Pakistan game da aikin binciken na duniyar wata mai tarihi. Kasar Sin ta kuma karfafawa masana na gida da na waje gwiwar yin hadin gwiwa a nan gaba.
Ya ce, na’urar Chang’e-5 ta shiga matakin binciken kimiya, bayan da bangaren sauka na nau’urar dauke da samfura ya sauka lami lafiya da safiyar yau a yankin arewacin kasar.
Jami’in ya kara da cewa, nan gaba za a nazarci kasar da aka dauko daga duniyar wata, don fahimtar yanayin duniyar wata. Haka kuma kasar Sin za ta raba samfurin kasar da sauran kasashe da kungiyoyi, a hannu guda kuma za a baje wani bangare na kasar don jama’a su gani.
Kana Wu Yanhua ya sanar a yau Alhamis cewa, kasar Sin tana shirin harba kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati guda hudu, a wani mataki na shirin da take na gina tashar binciken sararin samaniya cikin shekaru biyu masu zuwa.
Wu ya ce, akwai shirye-shirye guda 11 da aka tsara game da gina tashar binciken sararin samaniyar cikin shekaru biyun dake tafe, ciki har da gina sunduki da aka tsara harba shi a cikin watanni shida na farkon shekara mai kamawa, da dakunan bincike guda biyu, da kuma kambun sama jannai mai daukar mutum hudu da jiragen dakon kaya guda hudu.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)