Jiya Lahadi, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar ya kira taron manema labarai, inda jakada Liao Liqiang ya bayyana cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 ya zama wani muhimmin bangaren hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Masar ta fuskar yaki da annoba.
Kwanan baya, kasar Sin ta tsai da kudurin samar da taimakon allurar COVID-19 ga kasar Masar, da samar da sauki ga kamfanonin kasar Masar wadanda suke son sayan allurar da kamfanonin Sin suka samar.
Matakin ya nuna zurfin zumunci a tsakanin shugabanni da al’ummomin kasashen biyu, kuma Sin na fatan ba da taimako ga kasar Masar wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri. Kaza lika, kasar Sin za ta samar da wasu allurar rigakafin cutar COVID-19 ga ofishin sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta LAS.
A halin yanzu, kasar Sin tana samar da taimakon allurar rigakafin cutar COVID-19 ga kasashe masu tasowa guda 14. A nan gaba kuma, za ta samar da taimakon allurar ga sauran kasashe masu tasowa guda 38. Sin ta riga ta shiga cikin shirin “samar da allurar rigakafin cutar COVID-19” a hukumance, inda ta tsai da kudurin samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 guda miliyan 10 bisa wannan shiri, domin biyan bukatun wasu kasashe masu tasowa.
A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan kamfanonin kasarta, da su yi hadin gwiwa da kamfanonin kasashen ketare, domin nazari da kuma sarrafa allurar rigakafin cutar COVID-19, kuma tana goyon bayan kamfanonin da abin ya shafa, da su fitar da allurarsu zuwa kasashen duniya dake bukatar allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin gaggawa, da wadanda suka nuna amincewa kan allurar da kamfanonin Sin suka sarrafa, da kuma wadanda suka ba da iznin amfani da allurar kirar Sin cikin kasashensu.
Liao Liqing ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen da abin ya shafa, musamman ma ga kasashe masu tasowa, domin ba da gudummawa yadda ya kamata a fannin kiwon lafiyar dukkanin bil Adama. Kuma, tana fatan gamayyar kasa da kasa za su dukufa, tare da daukar matakai yadda ya kamata, na raba allurar rigakafin cutar COVID-19 tsakanin kasa da kasa cikin adalci, ta yadda za a kawo karshen yaduwar cutar a kasashen duniya cikin sauri. (Mai fassarawa: Maryam Yang)