Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana kudirin kasarsa na taimakawa sama da kasashen Afirka 19 da alluran rigakafin COVID-19, da ma hadin gwiwar Sin da kasashen duniya kan samar da alluran rigakafi, ta yadda alluran rigakafin da ta samar, zai kasance kayan al’ummar duniya baki daya.
Wang ya bayyana haka ne, lokacin da aka bukaci ya mayar da martani kan kalaman da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a yayin taron tsaro na Munich cewa, ya kamata Turai da kasar Amurka, su samar da isassun alluran rigakafin COVID-19 ga nahiyar Afirka, idan ba haka ba, kasashen Afirka za su iya zaben sayan alluran rigakafin daga kasashen Sin da Rasha, yana mai cewa, “karfin kasashen na yamma zai kasance bisa manufa, ba wai a zahiri ba”. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)