Sin Za Ta Taimakawa Bankin Musulunci Wajen Gina Dakunan Gwajin Lafiya

Daga CRI Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniya da bankin musulunci na (IsDB) a jiya Litinin, inda zata taimakawa bankin wajen gina dakunan gwaje-gwajen lafiya a mambobin kasashen don yaki da annobar COVID-19.

Chen Weiqing, jakadan kasar Sin a Saudiyya kana wakilin kasar Sin a kungiyar hada kan musulmi ta (OIC), tare da Mansur Muhtar, mataimakin shugaban bankin IsDB, sun sanya hannu a madadin bangarorin biyu a Jeddah, na kasar Saudiyya.

Chen ya ce, hadin gwiwa shi ne hanya mafi dacewa wajen yakar annoba. Kasar Sin da kasashen musulmi suna taimakawa junansu wajen yaki da annobar cutar numfashi.

Ya ce ya yi amanna za a iya cimma nasarar kawar da cutar COVID-19 ta hanyar yin kokarin da kasar Sin da kasashen musulmi da kuma kasa da kasa suke yi.

Mansur Muhtar, ya bayyana godiya ga kasar Sin bisa yadda take bayar da taimako ga mambobin kasashen musulmi na IsDB masu karamin karfi wajen yakar annobar.

Mansur ya ce, yana la’akari da wannan hadin gwiwar a matsayin mafari, kuma yana fatan za a ci gaba da karfafa hadin gwiwa da yin cudanya tsakanin kasar Sin da bankin a fannoni da dama karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa.(Ahmad Fagam)

Exit mobile version