Sinawa Ba Za Su Manta Da Danyen Laifin NATO Na Kai Wa Yugoslavia Hari Ba
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sinawa Ba Za Su Manta Da Danyen Laifin NATO Na Kai Wa Yugoslavia Hari Ba

byCGTN Hausa
1 year ago
Sinawa

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka yi yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya mayar da martani game da batun harin da kungiyar NATO ta kai wa Yugoslavia, inda ya bayyana cewa, al’ummun Sinawa ba za su manta da wannan danyen laifin da NATO ta aikata ba.

Lin Jian ya yi nuni da cewa, “Kafin shekaru 25 da suka gabata, rundunar sojojin NATO dake karkashin jagorancin kasar Amurka ta kai wa jamhuriyar tarayyar Yugoslavia, wadda kasa ce mai mulkin kai hari daga sama ba tare da samun iznin kwamitin sulhun MDD ba, harin da ya haddasa mutuwar dubban fararen hula, ciki har da ‘yan jaridar kasar Sin guda uku. Al’ummun Sinawa ba za su manta da wannan danyen laifin da NATO ta aikata ba har abada. Kuma ba zai yiwu su yarda a sake aikata irin wannan laifin ba. Bangaren Serbia da ofishin jakadancin kasar Sin dake Serbia su kan shirya ayyukan tunawa da lamarin a kowace shekara.”

Kana rahotanni sun nuna cewa, kwanan baya shugaban Paraguay Santiago Peña Palacios ya gayawa manema labaran kasar Japan cewa, kungiyoyin aikin gona na kasarsa sun bukace shi da ya kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva shi ma ya dade da gabatar da shawarar cewa, ya dace Paraguay ta kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin. Game da wannan, Lin Jian ya bayyana cewa, “Nacewa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, matsaya ce da aka cimma a fadin duniya, muna fatan shugabannin kasashen da abin ya shafa su bibiyi tarihi kuma su bi burin al’ummomin kasa da kasa, haka kuma su yi zabin da ya dace, ta yadda za su tsai da kudurin da zai dace da babbar moriya mai dorewa ta kasashensu.” (Mai fassara: Jamila)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Za A Samu Kyautatuwar Hadin Gwiwar Dake Tsakanin Sin Da Faransa

Za A Samu Kyautatuwar Hadin Gwiwar Dake Tsakanin Sin Da Faransa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version