CRI Hausa" />

Sinawa Dake Najeriya Sun Yi Kira Da A Hada Kai Don Tinkarar COVID-19

Jiya Talata, kungiyar hadin kan kamfanonin samar da kayayyakin masana’antun kasar Sin dake Najeriya ta ba da wata takardar shawara a Abuja, hedkwatar mulkin Najeriya, zuwa ga kamfanonin Sinawa dake kasar, inda ta yi kira da su dauki matakan tinkarar cutar COVID-19 yadda ya kamata, sannan kuma da sauke nauyin dake wuyansu na taimakawa al’ummar Najeriya wajen yakar cutar, ta hanyar samar da gudummawar kudi da kayayyaki.

Takardar ta nuna cewa, “dangantakar kasashen biyu na cikin lokaci mafi kyau a tarihi. Bayan bullar wannan cuta a kasar Sin, shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnati da kuma jama’ar Najeriya na goyon bayan kokarin da kasar Sin ke yi na tinkarar cutar. A halin yanzu, yaduwar cutar ya ragu matuka a ciki kasar Sin. Yanzu haka Najeriya tana fuskantar irin halin da Sin ta shiga a baya, a don haka, kamata ya yi, mu taimaka ba tare da bata lokaci ba.”
A shekarar 2019 ne, kamfanoni masu jarin kasar Sin suka kafa wannan kungiya mai mambobi 21 kuma ita ce kungiya irin ta ta farko da Sinawa dake tsakiya da arewacin kasar Najeriya suka kafa. (Mai Fassarawa: Amina Xu)

Exit mobile version