Connect with us

DAGA NA GABA

Sir Ahmadu Bello Sardauna: Gwarzonmu Na Mako

Published

on

Sir Ahmadu Bello Sardauna: Gwarzonmu Na Mako

 

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto:

An haifi Sir Ahmadu Bello a watan shida na shekarar 1910 a garin Rava da ke garin Sakkwato. Ahmadu Bello xa ne ga hakimin Rava Ibrahim.  Shi kuma Ibrahim xa ne ga sarkin musulmi na bakwai Abubakar Atiku shi kuma Abubakar Atiku xan sarkin musulmi na farko ne Sultan Bello. Sultan Bello kuwa xan mujaddadi Shehu Usmanu ne wanda ya kafa daular muslunci mafi faxi da girma a yankin qasashen Afrika.

Kamar kowanne xan musulmi Sir. Ahmadu Bello ya fara da karatun allo sai ilimin littattafan addini a shekarar 1917-1926. Ya halarci makarantar lardi ta Sakkwato ( Sokoto Middle School) Daga nan ya tafi makarantar horas da malamai ta Katsina ( Katsina teachers training college). Bayan ya kammala cikin shekara biyar a makarantar horas da malamai ta Katsina sai sarkin musulmi ya ba shi aikin koyarwa a tsohuwar makarantar da ya bari (Sokoto middle school)

A shekarar 1934 aka yi masa naxin hakimin garin Rava. Bayan shekara huxu masarautar sarkin musulmi ta qara masa girma da sauyin aiki zuwa garin Gusau. A shekarar 1938  ne ya shiga cikin ma su takarar neman sarkin musulmi wanda Allah bai sanya ya yi nasara ba. Sarkin musulmi Abubakar na uku bayan samun nasararsa babu daxewa ya yi wa Sir Ahmadu Bello sarautar Sardaunan Sakkwato.

Sardaunan Sakkwato ya tsunduma kansa a siyasa sosai a shekarar 1945 ya taimaka wajen kafa (Youth social circle) wadda a shekarar 1948 ta narke a cikin jam’iyyar mutanen arewa NPC (Northern People Congress) wacce ya zama shugabanta a shekarar 1954. A shekarar 1948 ne ya sami damar halartar wata horaswa ta musamman kan sha’anin gudanar da mulkin qaramar hukuma (local government administration) a qasar Ingila.

Bayan dawowarsa gida Najeriya daga Ingila an wakilta shi ya wakilci lardin Sakkwato a majalisar wakilai ta lardi. An kuma zave shi a matsayin xan majalisar wakilai. Shi ne xan majalisar da ya fi kowanne jajircewa kan duk wani abu da ya shafi ci gaban arewa. Babban abin da Gamji ya fi sanyawa a gaba shi ne, ganin ‘yan kudancin qasar nan bas u danne ‘yan arewa ba , da tuni suka sha gaban ‘yan arewa a wajen ilimin zamani saboda rashin rungumar ilimin zamani da ‘yan arewa ba su yi da wuri ba. Sir Ahmadu Bello yana cikin wakilan arewa da suka tsara kundin tsarin mulki na farko. A zaven da aka yin a shekarar 1952 sir Ahmadu Bello ya sami nasarar zama xan ajalisar wakilai na arewa , sannnan ya zama ministan ayyuka da ministan kyautata al’umma sai ministan N.A. A shekarar 1954 kafin mulkin kai ya zama Firamiyan arewacin Najeriya.

A shekarar 1957 ya jagoranci wakilan arewa zuwa London domin tattaunawa kan batun samun mulkin kai . A zaven da aka yi na samun mulkin kai a shekarar 1959 sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya zama shugaban jam’iyyar N.P.C ya lashe mafi rinjayen kujerun majalisar zartaswa. Da haxin gwiwar jam’iyyar NCNC wadda Dr Nmandi Azikwe ya ke jagoranta suka samu yancin kai. Qaunarsa da ci gaban aewacin Najeriya ya sanya ya janyewa Sir Abubakar Tavawa Valewa ya zama Firamiya arewa domin ya ci gaba da tsara ayyukan ci gaba a arewacin qasar nan. Sannan bai son zaman garin Lagos ba ya buqatar nisa da lardin arewa , wannan ta sanya masu fashin baqin siyasa suke yi wa sir Ahmadu Bello kallon mutum maras kwaxayin duniya da mulki.

Kasancewarsa firamiyan arewa kwalliya ta biya kuxin sabulu , a lokacinsa ne ya samar da:-

Northern Regional Development corporation (NRDC)

Northern Nigerian Development Corporation (NNDC)

Bank of The North

Broadcasting company of Northern Nigeria (BCNN)

Nigerian Citizen Newspapers.

 

Lokacin da ya zama firimiyan arewa kudancin qasar nan ta yi wa arewa nisa wajen qarfin tattalin arziqin qasa. Sir Ahmadu Bello ya tsaya kai da fata kan dole sai arewa ta kamo kudancin qasar nan ta zarce , musamman ganin irin arziqin da ke jibge a  arewacin qasar nan. Wannan tasa Sir Ahmadu Bello ya zamana ba dare  ba rana yana tafe  domin jin matsalolin arewa da buqatunsu kowanne lokaci yana kan hanyar ziyartar arewacin qasar nan domin jin matsalolinsu da buqatunsu da kuma irin arziqin da Allah ya hore musu. Bisa wannan dalili ya xauki guraben tabbatar da tsarin noma da kiwo ya koma irin na zamani. Ya kafa masana’antu domin samar arziqi ga arewa da kuma samar da aikin yi ga mutanen arewa. Sir Ahmadu Bello ya gayyato Turawa da Larabawa daga qasashen waje domin su kafa masana’antu a yankin arewa domin samar da arziqi.

Qarancin ma’aikatan arewa a ma’aikatar gwamnatin tarayya ya sanya Sir Ahmadu Bello ya dinga tura xalibai kwasa-kwasai domin cike guraben da su ke haqqin mutanen arewa ga ma’aikata ga arewa.

Rashin wadatar ilimi a yankin arewa ya sanya wasu guraben ‘yan kudu ne ke aiki duk kuwa da cewa ‘yan arewa ne ke da haqqin yin waxannan ayyukan. Ga hange da faxin qirji irin na Sardauna ya lura cewa ga dukkan alamu ‘yan arewa sun gama bauta qarqashin Turawan mulkin mallaka , ga wata kuma sabuwar bautar za su fara qarqashin ‘yan’uwansu ‘yan kudancin qasar nan. Wannan bauta kuma za ta fi wulaqanci da qasqanci da ciwo. Wannan ya sa sardaunan na Sakkwato ya tashi tsaye qarqashin shirinsa na (Northernization Policy). A bisa wannan  tsarin na  Northernazation Policy shi ne ciin hanzari a ilmantar da matasa waxanda za su cike gurbin duk wani aiki da ake buqata , bisa wannan tsarin an shiga lunguna an gina makarantu.

Sir Ahmadu Bello sardaunan Sakkwato ya sanar da makarantun yaqi da jahilci a karo na farko ga manya da tsofi, an samar da babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Sai nan da nan ilimi ya fara bunqasa a arewacin Najeriya , aka fara maye gurbin ma’aikatan nan da ‘yan arewa sannan aka fara cike gurabenmu na gwamnatin tarayya.

Bisa wannan dalili ne ya sanya wasu sojoji marasa tarbiya suka kashe shi a ranar 15 ga Janairu, 1966 bisa dalilin wai yana fifita arewa akan kudu. Sannan kuma yana son ya musuluntar da kowa , kuma kamar yadda su ka faxa wai ya cika varnar kuxi sannan ya haifar da qabilanci da wariya.

Allah sarki bayan kashe sardauna da ‘yan watanni kaxan suka fara gane kuskuren da su ka tafka.

Allah ya ji qan Sir Ahmadu Bello Allah ya yafe ma sa kurakurensa, amin.

 

An ciro wannan tarihin ne daga littafin Alfanda Amadu wanda fasihan marubutan nan biyu suka haxu suka wallafa Aminu Ladan Abubkar (Alan Waqa) da Auwalu Garba Xanborno a shekarar 2016.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: