Abba Ibrahim Wada" />

Sir Alex Na Son Solkjaer Ya Zama Kociyan Manchester United

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sir Alex Ferguson, na son kungiyar ta tabbatar da Ole Gunner Solkjaer a matsayin kociyan kungiyar na din-din-din.
Solkjaer dai yadawo da daraja da martabar kungiyar tun bayan da kungiyar ta kori Jose Mourinho ta bashi ragamar kungiyar a matsayin rikon kwarya kuma ya samu nasara a wasanni 11 cikin wasanni 13 daya jagoranci kungiyar.
Kociyan ya kuma jagoranci Manchester United ta doke kungiyoyin Arsenal da Chelsea a gasar cin kofin kalubale na FA kuma yanzu kungiyar tasa tana mataki na hudu akan teburin gasar firimiya.
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino shine kociyan da yake takara da Solkjaer wajen neman aikin kungiyar sai dai yanzu Sir Alex ya shawarci kungiyar data gwada Solkjaer.
Har ila yau, Sir Alex yana fatan kungiyar zata dauki matakin tabbatarwa da Solkjaer kujerar tasa domin ‘yan wasan kungiyar su samu nutsuwa sannan shi kansa Solkjaer zai fara shirye shiryen kakar wasa mai zuwa.
Sir Alex dai ya jagoranci Manchester United ta lashe gasar firimiya 13 acikin shekaru 27 da yayi yana koyar da kungiyar sannan kuma yayi amanna da yadda Solkjaer ya samu mataimaka na gari wadanda zasu rika bashi shawara.

Exit mobile version