Connect with us

KIWON LAFIYA

Sirrikan Jikin Mutum (2)

Published

on

‘Yan uwa Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barka mu da sake saduwa a wannan shafi da ke zakulo bayanai domin ku fa’idan tu, ku san yadda jikkunan ku ke aiki.
Makon da ya gabata, na tsaya a inda nake cewa:
Da akwai wata dadaddiyar al’ada ta. Dan adam wadda a wannan nahiya tamu take fuskantar kalu bale mai yawa. Wannan al ada tana daya daga cikin sirrikan da suka sa dan adam ya yi sauran dabbobi fintinakau, saboda wannan al ada ce ta gina wa dan adam kwkwalwar sa, ta cika ta da hikima da hankali, da ikon gane daidai da akasin daidai. Ko zaku iya canka wannan wacce al ada nake nufi? To idan kun bani gari ga amsa: Karatu! Tun da Allah ya halicce ni ban taba ganin tinkiya ta dauki takarda domin tayi karatu ba, sai domin ta ci. Hanyar Karatu ita ce hanya daya tilo ta samun ingantacccen ilimi wanda zai gina kwayoyin kwakwalwar ka/ki, ya bunkasa sadarwa a tsakanin su, tare da kaifafa yanayi da karfin aikin su. Duk wanda baya karatu, to ban da shi a wannan gwaggwabar garabasa.
Masana tunanin dan adam sun ce mutum ko da takardun da ake zubar wa a shara yake dauka ya karanta, kuma ya fahimta, hakika kwakwalwar sa zata sauya. Abin da ba a sani ba dangane da kwakwalwa da yadda take aiki, yafi Abin da aka sani yawa, ko ince ya nunnunka shi. Nazari akan kwakwalwa ya bude wa malaman kimiyya kafofin gano abubuwa da dama game da yadda jiki na da naaka ke aiki. A wasu lokutan ana amfani da kwakwalwar mutum yayin nazarin, a wasu lokutan kuma, akan yi da ta dabbobi kamar su biri da bera.
Kwakwalwar mutum gwana ce wajen fassara zafin ciwo ko radadi a wani sashe na jiki. Amma abin mamakin shi ne ita akan kanta, kwakwalwa bata jin wannan zafi ko ciwo da kake ji a wannan sashe. Ana nan ana ta bincike domin gano dalilin hakan.
A kowanne lokaci, wannan halitta da ke cikin kokon kan mu cikin aiki take, kwakwalwa bata hutawa, cikakkiar hutawa; sai ranar da mutum yayi bankwana da duniya. Wani zai tambaya: shin kwakwalwa bata hutawa yayin da nake bacci, ko kuma na zauna ina hutawa ko shakatawa? Amsar ita ce: E, bata hutawa, sai dai yawan ayyukan da take yi yana raguwa ainun yayin da mutum ke bacci.
Mu dauki misali cewa ka zauna kana hutawa; a daidai wannan lokaci, ya danganta da irin zaman da kayi. Abin da ke faruwa shi ne: kwakwalwa tana bada umarni ga wasu gabban su sakata su wala, a lokaci guda kuma tana bada umarni ga wasu gabban su takure, saboda kawai a baka dama kayi irin zaman da kake so. A wani zaman, za a sassauta tsokokin cinyar ka na baya, sannan a takura ‘yan uwansu na gaba dake cinya.
Da ni, da kai, da kowa ma, Ubangiji ya halitta mana kwakwalwa saboda muyi amfani da ita wajen bin hanyoyin da zasu inganta rayuwar mu. Sai dai kash! Da yawan mutane basa amfanuwa da wannan baiwa ta hanyar da ta dace. Akwai wani sirri da ya kamata mu sani: girman kwakwalwa ya banbanta daga mutum zuwa mutum, kamar yadda muke iya gani a waje, girman kawunan mu ba daya bane, wani yana da katon kai, wani madaidaici, wani kuwa karami. Tambayar anan shi ne, me ya ke banbanta tsakanin kwakwalwar wannan da wancan?
Kamar yadda na taba fada, kwakwalwa na da kwayoyin halitta da ake kira “neurones” wanda yawansu ya kai biliyan tamanin da shida (86 billion neurones). Wadannan kwayoyin halittu na musayar sako a tsakanin su, sannan daga lokaci zuwa lokaci, ana samun kulluwar sababbin alaka a tsakanin “nueurones”, wadda a da can babu ita. Wato “neurone” daga waje kaza zai kula sabuwar alaka da wani “neurone” a wani wurin a cikin kwakwalwa. Hakan na faruwa ne yayin da kwakwalwar ka/ki ta hadu da sabon abu.
Ga misali: yayin da ka ga sabuwar motar da baka taba gani ba, ko kika je wani gari wanda baki taba zuwa ba, ko ka ci wani abu wanda baka taba ci ba, duk wadannan sabbin abubuwa za a musu rajista a cikin kwakwalwar ku. Wannan shi zai sa a samu sababbin alakoki tsakanin neurones din. Saboda haka, iya yawan alakoki da kawancen da “neurones” ke dashi, iya karfin tunani ka/ki, da nazarin ka, da sanin ya kamatar ka, da sauran su.
Wadannan abubuwa shi muke cewa “edperiences”, watakila da hausa zan iya kiran sa da “kasantuwa”.Amma kar ku manta, akwai mummunar kasantuwa, akwai kuma kyakkyawar kasantuwa. Duk wanda ya faru ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ko kayi ta maimaita shi har aka dauki lokaci, to sai ya zama dabi’a. Shi yasa yake da kyau mutum ya san abubuwan da suka kamace shi, ya guji aikata munana, sannann yayi ta kokarin kyawawa. Saboda duk wanda aka maimaita sau wani adadi, kwakwalwa zata yi musu rajista ne, kawai sai su dinga faruwa ba tare ka kula ba, ko ba tare da ka tattara hankali wajen gudanar da aikin ba.
Abin da ke faruwa kenan ga wadanda suka saba da wani Abu: misali masu shan taba, shan giya, caca, da sauran su. Haka ma masu yi wa yara tsawa, da masu saurin fushi. Ban manta da masu motsa jiki ba, da masu yawan karatu. Halin kirki dabi’a ce, haka ma akasin haka. Kwarewa kan gudanar da wani aiki shi ma dabi’a ce. Amma hakan ba ya nuna cewa ba za’a iya sauya dabi’a ba. Ana sauya ta musamman daga mummuna zuwa kyakkyawa, sai dai bani da hurumin shig wannan fagge.
Wai shin kun san wannan sirrin na jiki kuwa? Ayyuka masu yawa da ake gudanar wa a jikin ka, ana amfani da kemikal ko kuma a samar dashi a sanadiyyar aiki. Akwai kemical da ake samarwa yayin da kika ji ciwo ko rauni, domin a rage ko a hana zubar jini. A bayanin da na bayar a baya kadan, akwai kemikal da suke taka rawa wajen samuwar alaka tsakanin kwayoyin halittar kwakwalwa. Akwai kemikal da ke taka muhimmiyar rawa wajen markada abinci, narkar da shi, da taskance abin amfanin da ke dauke da shi.
Bari kuji wani abun mamakin kuma. Akwai kemikal din da ke samuwa a kwakwalwa yayin da kake ko kike soyayya! Idan muka matsa gaba kadan, akwai kemikal din da kwakwalwar mu ke fitarwa yayin da muke farin ciki da murna da annashuwa. Wato jikin nan naka yana da ban ta’ajibi. Akwai kemikal kala kala da suke samuwa ta hanyoyi daban daban, amma mafi yawa bamu sani ba. Sarkin halitta Ya tsara halittar mu yadda baza su cutar da mu ba.
Bari in dan kara maka bayani kadan akan kemikal. Nasan kullum kana numfashi! To iskar da kake/kike shaka, da iskar da kuke fitarwa, dukkan su na dauke da kemikal. Shi kansa jikin na ka kemikal ne kala kala wadanda Sarki Buwayayye Ya tsara, Ya jera, Ya tankade, Ya rairaye, sannan Aka samar da ni da kai a matsayin halittar mutum. Shi yasa yake da kyau a ce muna ware lokaci musamman domin mu kalli jikin mu, ko mun tuna baiwar da Rabbana ya bamu. Ko alkur’ani ya kalubalance mu “ Shin ba kwa tunani ne?”
Mudan koma baya kadan. Ita wannan kwayar halitta ta kwakwalwa wato “neurone”, tana da matukar kankanta sosai. Yanzu zan baku misali wanda zaku sa a ma auni domin hasaso girman wannan kwayar halitta. Za a iya samun “dubbai” a gurin da bai fi girman ayar da na rubuta karshen wannan zance ba. Idan baka gane ba, ina nufin, “full stop” (.), guri daya da bai fi girman (.) ba, zai iya taskance kwayoyin kwakwalwa sama da dubu!
Da yawan mu dai munsan cewa dan adam wata halitta ce mai kai daya, mai hannaye biyu, mai kafafu biyu, mai hankali, da hikima fiye da dabbobi, mai tsarin hallitta da tsarin rayuwa wadanda suka sha banban da na saura halittu, mai idanu biyu, hanci daya, kunne biyu, sannan mai tafiya tsaye, akan kafafu biyu, mai gudanar da rayuwa a wuni, mai bacci da daddare, mai kula da abubuwan dake faruwa yanzu, da kuma kiyasta wadanda zasu faru nan gaba. Wannan shi ne kadan daga cikin siffofi na mutum.
Sai dai kash! Mutane da yawa basu san boyayyun siffofin da muke dauke da su ba. Dauki cinya a misali. Idan zan tambayi daya daga cikin ku, me da meye suka hadu sukayi cinya? Watakila a ban amsa da cewa: tsoka, kashi da jijiya. Amma amsar tayi kadan. Saboda idann muka dauki tsokar, za a dade ana bayani, haka kashi, haka jijiyar, haka hanyar jinin, haka rigunan da suke jikin tsokokin da saura bayanai. Karanta rubutu irin wannan yana da matukar alfanu wajen wayar da kai ka fuskanci waye kai, me jikin ka ke dauke da shi, sannan muhimmi kuma, ka ga Girman Shi Wanda YaYi ka.

Mu hadu a mako mai zuwa idan Sarkin ya kai mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: