Sirrin Da Ya Sa Akwa Ibom Ke Karfafa Noman Waken Soya -Amos

Waken Soya

Daga Abubakar Abba,

Mista Amos Udom, babban mai ba gwamna jihar Akwa Ibom don shawara a kan sa ido kan ayyukan na jihar ya sanar da cewa, Makarantar koyon aikin nona ta jihar mayar da hankali wajen  daga darajar noman  waken soya a jihar.

Ya kuma bukaci masu zuba  hannun jari a harkar noma da su hada hannu da gwamnatin jihar Akwa Ibom don bunkasa samar da abinci a jihar.

Mista Amos Udom, babban mai ba gwamna shawara a kan sa ido kan ayyukan, ya yi wannan kiran ne a  lokacin da ya kai wa Mista Arnold Smith, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Pandagric Nobum Ltd, ziyara a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

Ya kuma yi  kira   ga Gwamnatin Tarayya data  samar da masara wadatacciya   don a samar da  wadataccen abinci a kasar nan.

A cewarsa, tun da aikin noma abu ne mai kyau, jihar a bude take don kawance da gonar bisa la’akari da hangen nesan gwamnati na bunkasa noman abinci a jihar.

Babban jami’in ya karfafawa  manoman da kamfanoni kwarin gwaiwa da su samar da irin wadanan amfanin gona ta hanyar samar da  ingantaccen iri, samar da kayan aikin noma, horo, da sake horar da manoma na cikin gida, cikakkun shirye-shiryen da ake yi na wadanda ba su ba, da kuma samar da masanan gona don noman nunawa.

Udom ta umarci manoman yankin da su yi amfani da damar da za a basu na horaswa kan kyakkyawan tsarin gudanarwa domin su kafa kansu cikin kungiyoyin hadin kai da kuma  rungumar dabarun noma na zamani.

Mista Arnold Smith, Babban Jami’in Gudanar da Ayyuka, ya ce sun yanke shawarar shiga harkar noma ne a wani yunkuri na daukaka nahiyar Afirka daga kangin talauci da yunwa.

A cewarta, “ Muna da tsari guda bakwai, daya daga cikinsu shi ne,   muna kuma kikarin shigo da mutanen da suke harkar hada-hadar kayan aiki don su shigo cikin wannan tsarin domin mu taimaka wajan faduwar farashin”. ”

Ta tabbatar da cewa dandalinta ya yi amfani da siyarwar

kan layi yayin kulle kwayar cutar Korona,  inda ya kara da cewa, mun sami damar sayarwa, mun iya motsawa kuma mun samu kaso mai yawa na tallace-tallace kuma a  wannan dan gajeren lokacin, abin da muka sayarwa yana da yawa kwarai da gaske saboda wannan lokacin ne wadanda ba su san mu ba suka san mu.

A cewarta, Muna son gusawa gaba daga sabon abu zuwa na yau da kullun, kasancewar kasuwannin mu na bude ba su da tsari sosai, da kuma nisan zuwa kasuwanni, zuwa gare mu muna ganin wannan shine mafi alkhairin da zamu ci gaba, unda ta kara da cewa,  yawancin matasanmu yanzu suna aiki ne daga gida, ba su da lokacin zuwa kasuwa, yawancin iyayenmu mata, wannan shi ne mafi kyawun abin da kowa zai iya yi a yanzu.

Sanni-Banjo, duk da haka, ya ce babban kalubalen da ke fuskantar tallan na intanet shi ne gaskiyar cewa ba mutane da yawa ba ne ke iya amfani da yanar gizo, kudu kud ta hanyar yin amfani da yanar gizo.

Exit mobile version