Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADON GARI

Sirrin Iyayen Giji… MATA SAI DA ADO

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in ADON GARI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hakika a duk inda mace ta ke ’yar kwalliya ce. Adon mace ya na kara ma ta kwarjini. Ta hanyar kula da gidanta zuwa kanta kadai ya isa uwargida ta sami zuciyar mijinta.

A duk lokacin da uwargida ta tashi ta gabatar da sallar Asuba, to bai kamata a ce ta koma ta kwanta ba. Ta cna idar da addu’ointa kamata ya yi ta nufi dakin girki, don dafawa mai gida da yara abincin safe. Kafin ya tashi daga bacci ya zamana kin dora abinci. Idan ki ka dora, ba wai zama za ki yi ba, sai ki ba wa abincin lokacin.

samndaads

Ki yi Sauri ki tsaftace falonki da duk inda ki ka san maigidan zai shiga. Ki na yi ki na duba girki.

Da zaran kin kammala komai, sai ki zuba abinci a ‘food flacks’ ko mazubin da ya dace ki kai inda ku ke cin abincin ki jera. Sai ki yi sauri ki shiga wanka. Da ma kafin ki fito kin tanadi wutarki a kasko, wacce za ki sa turaren wuta.

Ya na da kyau ki koyawa yaranki hanzari da zafin nama a nan. Sai ki yi sauri ki shafa mai ki shirya ’yan makaranta. Ke ma ki gyara kanki ki shafa hoda da jambaki. Ki yi kwalliyarki ‘simple’ ba ta tashin hankali ba. Idan ki na da doguwar rigarki ki dauko ki saka. Ki tabbata ta kama jikinki sosai.

Uwargida ya na da kyau dinkin kayanki na tsakar gida ya bambanta da na fita unguwa. Idan da hali hatta kyau da tsadar na yiwa mijinki kwalliya ya fita daban. Idan babu kitso a kanki ki gyara gashinki sosai. Ki bi jikin ki da turare; kama daga na jiki zuwa na tufafi. Ya zama kina ta kamshi ko ta ina.

Yara sun gama shiryawa kin kawo turare irin na yara mai dadin kamshi kin fesa mu su. Idan kuma babu ’yan makaranta shikenan. Sai a je a tsashi maigidan cikin siyasa da kwarkwasa; ba da hayaniya ko kwaramniya ba.

Idan sai an kai ruwa bandaki da ma tuni ke kin kai. Idan kuma da ruwa a cikin, shikenan ya na tashi sai ya nufi wanka. Kafin ya fito kin gyara gadon da ya tashi, kin gyara dakin tsaf kin sa turaren wuta ko fureshina.

Idan mai zuwa office ne, kada a bar shi ya makara. Idan dan kasuwa ne ya na da kyau a ce kin san lokacin tafiyarsa. Duk dai abin da a ke ciki ya zama dole ki tsaftace jikinki kin yi kwalliya. Kin shafa fodarki mai kyau, wacce ki ka san ta karbe ki.

Sai ki saka jambaki, mai kyau ki sa kwalli ki yi jagira, idan ki na yi. Idan kuwa ki na da yawan gira sai ki taje ta ta yi kyau. Da ma kin saka doguwar rigar ki kin yi kyau.

Ki tabbata kina yawan shishshige ma sa wajen cin abinci ta yadda kamshin turarenki zai kama shi sosai. Wannan shi ne salon kwalliyar safe mai tamke zuciyar maigida.

In sha Allah za mu zo mu ku da irin shiga da kwalliyar da ya kamata maigidanki ya zo ya same kid a ita a mako na gaba.

Tare da

LUBABATU YA’U (AUNTY LUBABAH)GSM: 08039690509 lubabatuce@gmail.com

SendShareTweetShare
Previous Post

Sharhin Laliga: Wa Ta Gangano?

Next Post

Mu Koma Gona Domin Noma Tushen Arziki Ne, In Ji Baba Akuyum

RelatedPosts

Aure

Ba A Zama A Kashe Komai A Ce Aure Ake Jira –Hauwa Muhammad

by Muhammad
10 hours ago
0

Sau da yawa akan samu matan da kan zauna su...

Gyaran Jiki

Mutane Ba Su Da Hakuri A Gyaran Jiki, Sun Fi Son Sha-yanzu-magani-yanzu – Rabi Sule

by Muhammad
2 weeks ago
0

Gyaran jiki yana daga cikin sana’o’in da ke tashe a...

Hassana Hamisu

Shawarata Ga Matan Gida Da Ba Su Yin Sana’a – Hassana Hamisu

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

A koyaushe mata sukan yi kishin ‘yan’uwansu musamman ta fuskar...

Next Post

Mu Koma Gona Domin Noma Tushen Arziki Ne, In Ji Baba Akuyum

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version