Muhammad Auwal Tilde" />

Sirrin Sana’ar Tukin Keke Napep A Jihar Filato — Kwamared Dahiru Hassan

Sana’ar tukin Keke Nafef, sa’ana ce da dumbin matasan al’ummar wannan kasa ke cin abinci karkashinta. Wakilinmu MUHAMMAD AUWAL TILDE da ke Jos, ya samu tattaunawa Shugaban Kungiyar KOMRED DAHIRU HASSAN a kan wasu muhimman batu da suka shafi sa’anar kamar haka:

Ko za ka gabatarwa da masu karatu kanka?

Assalamu Alaikum, sunana Dahiru Hassan Shugaban kungiyar masu sana’ar tukin Keke Nafef (Tricycle Riders Union of Nigeria) a garin Jos na jihar Filato.

Bayan kwashe shekaru biyar da Gwamnatin Jihar Filato ta kaddamar da wannan kungiya  taku, ko za ka fada mana wani ci gaba da wannan kungiya ta samu?

To, Alhamdulillahi! Ko shakka babu mun  sam ci gaba matuka gaya a wannan sana’a, don kuwa matasa da dama sun samu aikin yi sun daina zaman banza, mun kuma samu sauki kawarai da gaske a bangaren sufuri. Haka zalika, wani babban ci gaban da muka sake samu shi ne na zaman lafiya, don kuwa Allah cikin ikonSa, Ya sa mun sadaukar da kanmu domin mu tabbatar an samu zaman lafiya.

Akwai wani lokaci da aka samu hatsaniya mutanen da ke a Unguwar Rububa ba sa iya zuwa kasuwar Taminos da ke Nassarawa, sai dai su yi zagaye. Wannan dalili ne ya sa dole ne mutane sai sun hau abin hawa biyu ko uku kafin su kai ga kaiwa wannan kasuwa. Ganin haka ne yasa mu Shugabanni muka zauna muka tattauna muka kuma ga dace cewa, mu musulmai wadanda ke aiki a wannan Tasha ta Taminos, mu rika daukar fasinjan Unguwar Rukuba mu bi ta Nassarawa tunda Unguwa ce ta musulmai, daga nan sai mu zo mu mika su ga membobimmu da ke  unguwar Rukuba jakcan su karasa da su zuwa Unguwanninsu.

Da taimakon Allah da gudunmawar da jami’an tsaro ke bayarwa, mun ci nasara kwarai da gaske. Saboda mu a aikimmu ba ma nuna banbancin addini ko kabila, dokar kungiyarmu ta haramta wannan kacokan. A ko’ina kake idan ka shigo wannan kungiya za mu karbe ka hannu biyu-biyu tare da tabbatar da cewa mun kare hakkinka da kuma mutuncinka. Babu shakka mutane sun samu saukin zirga-zirga daga gidajensu zuwa wurin kasuwancinsu da sauran sana’o’insu. Haka nan wannan ya sa mutane sun samu sauki wajen jigilar kayansu  zuwa inda suke so su kai ba tare da wani bata lokaci ba.

Wannan ya taimaka ainun wajen tsare rayukan al’ummar da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, sakamakon tashe-tashen hankula da aka rika samu a baya a jihar ta Filato, hakan ya kawo fahimta a tsakanin al’umma inda muka hada kai da jami’an tsaro muna aiki kafada da kafada wajen tabbatar da zaman lafiya. Hakan yasa na yi ta samun kyaututtukan yabo daga kungiyoyi daban-daban na ciki da wajen kasar nan.

Haka zalika, ina daya daga cikin Shugabannin da suke jagorantar kungiyar kuma har lokacin da aka ce za a hana aiki da Babura, tare da ni aka zauna da kwamitin da gwamnati ta kafa don a dubi yadda za a tsara yin aiki da keKe Nafef din da gwamnatin jihar ta yi  odar su don gudanar da harkar sufuri a cikin garin Jos da kewaye  ba tare da samun wasu korafe-korafe kan kasha-kashen masu tukin Babura a jihar ba.

Har ila yau, Kasancewata na daya daga cikin ‘yan kwamatin, nan take na shaida masu cewa, akwai baba-gari da suke ci ga da sana’ar kawai don cimma burinsu na sace-sacen Babura kuma suna samun daurin  gindin zama ne saboda rarrabuwar kawuna da ake samu a wajen masu sana’ar tukin baburan, wanda sanadiyar hakan tasa aka samu jagorori daban-daban a cikin kungiyar a nan cikin garin Jos da kewaye da hakan ya bawa bata gari samun gindin zama suna aikata laifuffuka iri daban-daban. Idan wadannan bata gari suka aikata laifi a wannan bangare na Shugabanci, a kan kama su a ladabtar da su s sa su koma wancan bangaren na Shugabanci su yi rijista, su ci gaba da sana’arsu ba tare da sanin Shugabannin wannan bangaren ba sai su karbe su hannu biyu-biyu su yi musu rajista.

Ba alfahari ba, a garuruwan Jos da Bukuru ne a wannan jiha kadai za a samu membobin kungiya masu bin doka da oda wajen yi wa gwamnati da’a. Haka nan a duk manyan biranen kasar nan, zan iya bugun kirji in ce kusan duk Nijeriya babu membobin wata kungiya da take yi wa gwamnati biyayya kamar membobinmu, hatta kungiyar matuka motoci ba sa bin doka kamar yadda namu membobin suke bi. Yanzu haka da nake yin magana da kai babu wani Keke Nafef da za a kawo daga wata jihar a zo a yi amfani da shi a nan garin Jos, ba tare da an yi masa rajista da fentin da gwamnatin jiha ta ba mu umarnin yi ba.

Gwamnatin da ta gabata ta sayo sabbin Keke Nafef ta raraba wa membobinku, ko kekuna nawa ne ta raba muku sannan yawanku ya kai nawa yanzu?

Ko shakka babu, gwamanatin da ta gabata ta sayo kekuna guda 500 ta damka mana, kuma a wancan lokacin ‘yan kasuwa su ma sun sayi Babura 2000 sun kara damka mana, wasu daga cikin su sun sayi Kekuna guda 50 zuwa 200 suka ba mu. Bayan an kaddamar da mu mutane suka ga sana’ar tamu tana da kyau, suka yi ta sayen Baburan suna ba wa masu sha’awar shiga cikin harkar tukin Keke Nafef din, hatta manyan masu kula da harkar tamu sai da suka sanya hannun jarinsu a ciki, suka kara sayo wadannan Kekuna suka yi ta baiwa masu bukatar yin aikin tukin.

A yanzu haka da nake magana da kai an yi wa Keke Nafef rajista kimanin 17,600, kazalika matasa ne kaf ke aiki da su. Sannan duk Keke guda daya kusan mutane ne biyu ko uku suke cin abinci da shi, idan wannan ya gaji wannan ya karbe shi. Idan ka lissafa za ka ga akwai sama da 36000 da suke cin abinci ta wannan hanya ta Keke Nafef, sannan mafiya yawan su Magidanta ne.

Yaya dangantakarku da ta masu saya muku wadannan Keke Nafef take?

Godiya ta tabbata ga Allah! A nan masu hannun jari a wannan harka, mutane ne da suka amince mana, dalili kuwa tun a fari da aka kaddamar da mu suka gwada mu suka ga ba mu ha’ince su ba. Shi yasa suka yarda da mu suka ba mu hadin kai kuma mafiya yawa daga cikin su masu kudin gaske ne day a hada da maza da mata a cikin harkar. Saboda haka akwai kyakkyawar alaka tsakaninmu da su.

Wane irin kalubale kuke samu a cikin tafiyar?

Mun sami kalubale mai yawan gaske, amma kawai zan fadi muhimmai daga cikin su. Na daya dai akwai wani karfe da membobinmu suka makala a jinkin Baburansu don tsare lafiyarsu, amma sai masu motoci suka kai kukansu ga Hukuma suna so a tilasta mu mu cire wannan karfe. Abu na biyu kuma shi ne, mafiya yawan kayan gyaran Keke Nafef din nan jabu ne ba masu inganci ba, sakamakon cewa ba asalin na kamfanin da ake yin Baburan ba. Sannan kuma sai dan saba’nin da ake samu tsakanin masu Babura da masu tukinsa, wani lokaci mai Babur ya ce ba a gama biya ba, shi kuma mai tuki ya ce ya kammala biya. Daga nan ne za a yi bincike har a gano mai gaskiya. Sai kuma maganar Lasin da Gwamnatin Jihar ta nemi mu rika biya kamar yadda matukan motoci ke biya, inda a karshe muka ki yarda da wannan saboda mun lura baya kan doran doka musamman na jihohi. A karshe dai dole sai da ma’aikatar sufuri ta nemi mu yi zama da ita, muka zauna daga karshe ta amince za ta ba mu Lasin da famit kamar yadda ake a yi a wasu jihohi.

Akwanakin baya Kwamishinan ma’aikatar sufuri na wannan jiha, Honorabul Muhammad Ahmad Nazifi, ya ce gwamnati za ta kafa ma’aikatar da za ku yi aiki a karkashinta domin tsabtace wannan aiki naku, yaya ka kalli wannan batu na Kwamishina?

Mu a kungiyance muna aiki kafada da kafada da gwamnati, amma wannan harkar aikin namu kasuwanci ne kuma kowa ma zai iya shigowa ciki. Idan har gwamnati ta amince kamar yadda Kwamishina ya fada cewa, ma’aikatar sufuri ta san da zaman duk wata kungiya da ke gudanar da harkokinta a karkashi ofis dinta na wannan jiha.

Kafin mu kammala wannan hira zan so ka fada wa masu karatu yadda  ka ji labarin sake zaban  Barista Simon Bako Lalong, a karo na biyu. Musamman yadda wasu ke ganin bai yi wani abin a zo a gani ba a wa’adin mulkinsa na farko.

Sake zaben Gwamana Lalong, a karo na biyu bai ba ni mamaki ba, domin kuwa ya cancanci a sake zabensa musamman idan aka yi la’akari da irin rawar da ya taka wajen maido da jihar kan turbar zaman lafiya da yawon bude ido.

Yanzu haka akwai wurin shakatawa da gwamnatinsa ta kaddamar akwanakin baya, a tsakanin Unguwannin Kiristoci da Musulmai, wannan ko shakka babu ya kara jaddada zaman lafiya da yake kokarin maidowa wannan jiha.

Wannan wurin shakatawa mai suna (Forgibeness Centre), wato cibiyar yafewa juna, ta samu karbuwa daga wurin kabilu daban-daban da ke zaune a wannan jiha. Dalili kuwa, babu dare babu rana masu addinai daban-daban na tururuwar zuwa wannan waje su huta tare da abokansu, su sayi abinci da sauran abin sha hankali kwance ba tare da wata fargaba ba.

Exit mobile version