Sirrin Zama Sarauniya A Zuciyar Miji

Miji

Tare da Hafsat Mohammad Arabi,

Assalamu Alaikum! Barka da sake kasancewa da ni a wannan shafin wanda ke zakulo matsalolin ma’aurata tare da kawo shawawari dan magance su. A yau babban darasinmu zai tattauna ne a kan ABUBUWAN KULAWA GA MATA Burin kowace ‘ya mace ne a ce tana da guri na musamman a zuciyar mijinta, ta kuma kasance Sarauniya a gurin mijinta. Sai dai ‘yar uwa hakan ba ta faruwa ba tare da kin yi kokari kin zama cikakkiyar mace ba ta hanyar kulawa da kanki.  Muddin mace ba ta san kanta ba, ba ta samun wannan gurbin, shi ne za ku ga mace ta rasa me take ma mijinta duk yabi ya nesance ta, yake nuna mata Gadara da Isa, komai ta yi ba ta burge shi sai dai ya ga laifinta. To, ga duk wacce take da irin wannan matsala, ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ki kula da su:

Tsafta: tsabta tana taka rawar gani sosai a bangaren zamantakewa ta ma’aurata. Yana da kyau mace ta zama tasan kanta ta kuma san abunda mijinta yake so dan shine farkon abunda ya kamata tayi inbaki san Mijinki da abunda yakeso ba to bazaki taba zama abunda kikeso ba. Bawai dan baya yaba kwaliyyarki ko baice ba saiki zama kawai shasha kina yini da zanin kirji ko kizauna kullum jiya a yau ba gyara ba komai ba ke tunda bai nuna damuwa shikenan saiki sake jiki kawai. To ba haka bane yar uwa hasalima Maza marasa complain sunfi lura da daukar matakin da baki sani sai sun aikata. Bazaki san da hakan ba sai ranar daya Auro wata me tsabtar da kula dashi tukunna zaki gane kuskurenki haka duk yadda zaki so gyarawa damar ta riga tabar hannunki. To a kula.

Rashin Wayewa da Ilmin Zamani : Wata macen sam bata da ilmin da zata tafiyar da mijin nata haka kuma rashin wayewa bazai barta ta nema hanyoyin da zata nema hanyoyin magance matsalolin gidanta ba. Wanda inda da wayewa da ilmi zata nema hanyoyin sanin abubuwa da zai kawo karshen matsalarta eg. Duk da social media akwai bad side haka akwai good side dan a wannan zamanin komai kakeso zaka samu. Misali kina da matsalar rashin iya girki ko iya girka abunda mijinki yakeso to tabbas zaki sama yadda zaki girka a social media both bideo da writing akwai girkuna sosai da abubuwa da dama. Dan inba ta gyara ba zai iya jawo mata raini da wulakanci sosai agun mijinta sai a kula.

Rashin Iya Kwanciyar Sunnah da Gyaran Jiki: Tabbas! idan akace Mace bata iya kisser kwanciyaba to shima akwai matsala babba musamman in yana da wata matar bazata iya samun kanshi ba. Haka ranar da yake dakinta bazata dunga ganin walwalarsa kamar inyana wajen abokiyar zamanta ba. Shiyasa yake dakyau kina zama cikin ‘yan uwanki mata kina tambaya da jin yadda suke tafiyar da zamantakewarsu dan samun Karin ilmi koki dunga research ba kizauna sai chat din banza ba. Haka Rashin gyara kanki ‘yar uwa babban kuskurene a bangarenki ace bazakina kula dakanki kisan me kike cikiba miji ya kusanceki yana jinki kamas! Ba Ni’ima ba komai ko kuma inya kusanceta ya dunga jin wari sakamakon cutar sanyi ko da sauransu wanda yana dakyau da kinji abu makancin haka kiyi kokari wajen neman Magani rashin Magance wannan matsalar kansa mijinki yayita kyarar ki da wulakanta ki kirasa gane kanki. Kisani akwai natural abubuwa da zaki dunga sha fruit da sauran su wanda insha Allahu a nedt Topic dinmu zan rubuto wasu daga cikin abubuwan kara Ni’ima da gyaran jiki.

Rashin ladabi da Biyayya: wannan yana faruwa sosai dan wata matar batasan ta tausasa kalamanta ga Mijinta ba idan zatai mishi magana ko abu kai tsaye take cikin gatsali haka kuma bai isa ya sa ta koya hana taba. To kisani ‘yar uwa inkina wannan mijinki bazai taba ganinki da daraja ko mutumci bas am.

Korafi da Rashin Hakuri: Tabbas! wasu matan basu san hakuri ba ga korafi da abu ya faru sai suyita mita. Wannan shima yana saurin rusa zamantakewa yana jawo wulakanci ga macen saboda bazai dunga ganinta kamar mara mutunci.

Exit mobile version